Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya ziyarci Yunnan domin ganin yanayin lardin gabanin bikin bazara
2020-01-20 09:46:31        cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, gabanin bikin bazara da ke tafe nan da 'yan kwanaki. Shugaban na Sin wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, ya isa lardin na Yunnan ne a jiya Lahadi, inda da yammci ya shiga kauyukan al'ummun Wa, dake garin Qingshui babban birnin Tengchong.

Shugaba Xi ya yi amfani da ziyarar tasa, wajen nazartar yanayin da ake ciki game da ayyukan yaki da fatara, tare da gabatar da sakon murnar sake zagayowar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta al'ummar Sinawa ga mazauna yankin.

Har ila yau shugaban na Sin ya ziyarci tsohon garin Heshun, wanda ke matsayin zango na tsohuwar hanyar siliki da ta hada Sichuan da Yunnan na kasar Sin da kasashen Myanmar da India, inda ya ganewa idanunsa halin da ake ciki game da musaya, da killace tarihi da al'adu, da yanayin kare muhalli, da muhallin halittu a hanyar mai dadadden tarihi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China