Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Alummar Afrika ta Kudu da Sinawa sun gudanar da bikin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin a Johannesburg
2020-01-20 10:14:53        cri

Daruruwan al'ummar Sinawa da ta Afrika ta Kudu daga bangarori daban daban ne suka hadu a filin taro na Nelson Mandela dake birnin Johannesburg a jiya Lahadi, domin murnar sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa.

An gudanar da wake-wake da raye-raye na kasashen biyu domin nishadantar da mahalarta. An gabatar da wasannin Kung Fu da na tsalle-tsalle da sarrafa jikin na Acrobatics da sauransu, wadanda suka samu yabo sosai daga masu kallo.

Nelly Msomi, daya daga cikin wadanda suka halarci bikin, ya shaidawa Xinhua cewa, ya ga rukunoni da yawa suna gudanar da wasanni, kuma sun ba shi sha'awa.

Ita kuwa Tania Singphi cewa ta yi, ta ga raye-raye da wake-waken wata al'ada da ba ta taba gani ba.

A nasa bangaren, jakadan kasar Sin a Afrika ta Kudu, Lin Songtian, ya ce bikin na da muhimmanci wajen kara gina dangantaka tsakanin al'ummar Sinawa da ta Afrika ta Kudu, sannan ya samarwa Sinawan dake kasar, damar more bikin sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China