Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan GDP din kowanne dan kasar Sin ya haura dala dubu 10, lamarin dake zaman babban ci gaba ga raya alumma mai wadata
2020-01-20 10:53:11        cri

Babbar magatakardan kwamitin raya kasa da yin kwaskwarima ta kasar Sin Madam Meng Wei, ta shedawa manema labarai a jiya Lahadi a nan birnin Beijing cewa, a shekarar 2019, yawan GDP din ko wane Basine ya haura dala duba 10, matakin da ya alamanta cewa, karfin kasar Sin da kuma karfin samar da kayayyaki na al'ummar Sinawa na kara samun karuwa, har ma matsayin zaman rayuwar jama'a na kara ingantuwa, abin da ya bayyana cewa, Sin ta samu sabon ci gaba kan hanyar zama kasar dake da kudin shiga mafi yawa a duniya. Ban da wannan kuma, ya kasance babban ci gaba ne da Sin take samu wajen raya al'umma mai zaman wadata. Amma, Meng Wei ta nuna cewa, yawan GDP din ko wane dan kasa a kasashe masu wadata ya kai fiye da dala dubu 30, hakan ya sa, har yanzu Sin ke kasancewar babbar kasa mai tasowa.

Meng Wei ta nuna cewa, bisa kididdigar da aka bayar a watan Disamban bara, tattalin arzikin kasar Sin na samun sauyi mai inganci, yayin da kuma aka samu kyautatuwa a fannonin samar da kayayyaki da sayayya da farashin kayayyaki da dai saruansu. Wadannan sauye-sauyen da aka samu na da alaka da jerin manufofin da gwamnatin kasar ke dauka, matakin da ya alamanta cewa, tattalin arzikin na da inganci sosai, kuma yana iya samun bunkasuwa ba tare da tangarda ba. Ta kara da cewa, ko da yake, ana fuskantar yanayi maras tabbas a gida da waje, amma an yi kiyasin cewa, tattalin arzikin kasar Sin zai samu ci gaba yadda ya kamata a shekarar 2020, saboda ganin sharuda masu kyau da tushe mai inganci da Sin take da su. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China