Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yang Jiechi ya halarci taron koli na Berlin kan batun Libya
2020-01-20 11:23:11        cri

Yang Jiechi, wakilin musamman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kuma darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiya na JKS ya halarci taron koli na Berlin dangane da batun kasar Libya.

A yayin taron, Yang Jiechi ya yi nuni da cewa, ya kamata a sanya babbar moriyar jama'a da makomar Libya gaba da kome yayin da ake daidaita batun kasar, da dakatar da musayar wuta nan take ba tare da bata lokaci ba. Ya kuma yi kira da a hanzarta komawa teburin shawarwari da aikin samar da sulhu. A cewarsa, wajibi ne a bada muhimmanci ga samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da Libya take ciki, a kuma tinkari rikicin yadda ya kamata. Wakilin na kasar Sin, ya ce kamata ya yi a kau da illolin da ke biyo bayan abkuwar rikicin Libya, a kuma dauki matakai daban daban wajen daidaita batun. Ya ce kasar Sin na tabbatar da adalci kan batun Libya bisa sanin ya kamata, tana kuma bin kundin tsarin MDD, kana tana girmama ikon mulkin kan kasar ta Libya, da 'yancin kanta da cikakkun yankunan kasar. Har ila yau, kasar Sin na tsayawa kan kara azama wajen daidaita batun Libya a siyasance, karkashin shugabancin MDD.

A yayin da ake gudanar da taron, Yang Jiechi ya gana da shugabar gwamnatin kasar Jamus madam Angela Merkel da sauran shugabannin kasashen Turai. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China