Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CMG ya kira taron watsa labarai kan bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin
2020-01-20 20:10:26        cri

Yau Litinin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG a takaice ya gudanar da taron watsa labarai kan "bikin wake-wake da raye-raye na murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin na shekarar 2020", inda aka bayyana cewa, bikin da za a shirya zai jawo hankalin masu kallo matuka bisa kirkire-kirkiren fasaha da dabarun salo daban-daban na watsa shirye-shirye.

Ban da babban wurin da za a watsa shirye-shirye a nan birnin Beijing, za a kebe wasu wurare guda biyu a birnin Zhengzhou na lardin Henai da babban yankin lardin Guandong-Hong Kong-Macao, kawo yanzu, an riga an samar da tsarin 5G a wuraren nan uku, kana za a yi amfani da fasahar 3D wajen kallo da ido kai tsaye, za kuma a gabatar da shirye-shiryen bikin kai tsaye ta fasahar VR a karo na farko. Ban da haka, za a watsa bikin ta fasahar 4K, ta hanyar daukar bidiyo da na'urorin zamani na musamman.

Wannan shi ne karo na farko da CMG zai watsa bikin ta fasahar 8K, kuma zai wallafa fim din bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin na shekarar 2020 a karo na farko. Kana kafofin watsa labarai sama da 500 na kasashe fiye da 170 ciki har da Amurka da Birtaniya da Japan da Rasha da Brazil da Singapore da Maleisiya da Thailand da Laos da sinimomin kasashe da yankuna sama da 20 za su watsa bikin ko fim din bikin kai tsaye.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China