Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban ICRC ya yi kira ga mambobin AU da su kara azama wajen martaba dokokin jin kai
2020-01-22 10:02:01        cri
Shugaban kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji ta ICRC Peter Maurer, ya jaddada kira ga jagororin kasashe mambobin kungiyar AU, da su kara martaba dokokin jin kai na kasa da kasa, ta yadda za a kai ga dakatar da yake-yake.

Peter Maurer, ya ce wajibi ne a aiwatar da dokoki da ka'idojin kare fararen hula a lokutan tashe-tashen hankula, tare da kandagarkin fantsamar rikici cikin al'umma, musamman a kasashen dake ba da gudummawar dakarun wanzar da zaman lafiya, dake aiki a sassan nahiyar Afirka.

Cikin wata nasarwar da ofishinsa ya fitar a jiya Talata, jami'in ya ce amincewa da aiwatar da yarjejeniyar dakile yaduwar makamai da mambobin AU suka yi, daya ne daga ginshikan dakile jin amon bindiga a nahiyar. A hannu guda kuma akwai bukatar magance dalilan dake haifar da tashe-tashen hankula daga tushensu a nahiyar.

Kalaman Mr. Maurer na zuwa ne, bayan kammala ziyararsa a yankunan kahon Afirka, da suka hada da kasashen Kenya, da Somalia, da Habasha, inda bayan hakan ne kuma ya yiwa kwamitin wanzar da zaman lafiya da tsaro na kungiyar AU karin haske game, da yanayin ayyukan jin kai da ake ciki bisa sakamakon ziyarar tasa.

kwamitin kasa da kasa na kungiyar agaji ta ICRC na gudanar da ayyukan jin kai da hadin gwiwar kungiyar AU, a wani mataki na ba da kariya ga fafaren hula dake rayuwa, a yankunan dake fama da tashin hankali, ciki hadda mata da yara kanana, da wadanda ke gudun hijira a cikin yankunan su, da 'yan ci rani da ake tsare da su, da wadanda suka bace, tare da kare fararen hula daga hare-haren ababen fashewa, a yankuna masu cinkoson jama'a.

Kungiyar AU ta yiwa shekarar bana take da shekarar "dakatar da harbe harben bindiga: samar da yanayi mai nagarta na ciyar da nahiyar Afirka gaba." (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China