Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadun Afrika suna taro a Habasha kan jadawalin taron kolin AU karo 33
2020-01-22 10:20:02        cri
A ranar Talata aka bude taron wakilan kwamitin dindindin PRC, na kungiyar tarayyar Afrika AU karo na 39 a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.

A karkashin jadawalin taron kolin AU karo 33, wakilan na PRC suna gudanar da taron wuni biyu, daga ranar 21 ga watan Janairu, karkashin taken taron wannan shekarar, "Kawar da amon bindiga: Samar da ingantaccen yanayi don bunkasa cigaban Afrika."

Jakadun mambobin kasashen AU da jami'an kungiyar ta Afrika mai mambobin kasashe 55, ana sa ran za su tattauna da kuma tsara rahoto, kana da shirya ajandar taron majalisar kolin AU karo na 36, wanda ya kunshi ministocin harkokin wajen kasashen mambobin AU, wanda za'a gudanar tsakanin 6-7 ga watan Fabrairu.

Batun dake sahun gaba cikin ajandar da za'a tattauna a taron shi ne, yin kwaskwarima game da tsarin hukumar AU da yadda yarjejeniyar ciniki maras shinge a tsakanin nahiyar wato (AfCFTA) za ta fara aiki.

A jawabinsa na bude taron, mataimakin shugaban hukumar gudanarwar AU, Kwesi Quartey, ya jaddada aniyar hukumar wajen yin aiki tare da kwamitin PRC, domin samar da cikikken hadin gwiwa wajen tafiyar ayyukan kungiyar tsakanin bangarorin biyu. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China