Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Majalisar dattijan Amurka ta yi watsi da bukatar jamiyyar Democrats na neman tsige Trump
2020-01-22 15:13:10        cri

Majalisar dattijan Amurka wadda jam'iyyar Republican ke da rinjaye a jiya Talata ta yi watsi da kudurori uku a jere wadanda jam'iyyar Democrats ta gabatar na neman izinin gabatar bayanan shedun da ake bukata don kada kuri'ar tsige shugaban kasar Donald Trump.

Kudurorin da shugaban masu rinjaye a majalisar dattijan Amurka Chuck Schumer ya gabatar, don yin gyare-gyare kamar yadda Republican ta nema wanda ya shafi batun shirye-shiryen tsige shugaban kasar.

A ranar Talata aka fara shirye-shiryen tsige shugaba Trump a hukumance, wanda majalisar wakilan Amurka da jam'iyyar Democratic ke da rinjaye ke zargin shugaban kasar da laifin amfani da karfin iko wajen kawo cikas ga harkokin majalisar.

Babban abin da za'a fi mayar da hankali a ranar Talata shi ne yin muhawara da kada kuri'ar neman fara shirye-shiryen tsige mista Trump. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China