Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya taya Sinawa murnar bikin bazara
2020-01-22 19:25:53        cri

A yayin da ake shirin bikin bazara na shekarar bera ta 2020 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ta bakin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya taya Sinawa murnar wannan gaggarumin biki, tare da mika gaisuwa da fatan alheri ga daukacin al'ummun kasar Sin.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, kasar Sin ta yi bikin murnar cika shekaru 70 da kafuwarta, babban sakamakon da al'ummun kasar Sin suka samu sun shaida cewa, kasar Sin ta samu hanyar raya kasa da ta dace da yanayin da take ciki. Ya kara da cewa, Najeriya tana martaba manufar kasar Sin daya kacal a duniya, kuma huldar dake tsakanin kasashen Sin da Najeriya ta samu ci gaba cikin sauri a bara, haka kuma sassan biyu sun samu nasarori daga duk fannoni yayin da suke gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu, hakan ya sa kasashen biyu samun sabbin damammakin samun moriya tare, hakika Najeriya tana farin cikin ganin kasar Sin ta samu ci gaba yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya ce, shekaru 20 ke nan da aka kafa dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen Afirka, yana kuma alfahari matuka da ganin yadda hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu ya samu ci gaba mai yakini, har ya kasance abin koyi ga sauran kasashe masu tasowa, tare da amfanawa al'ummomin Sin da Najeriya, bera dabba ce mai girma a cikin dabbobi sha biyu wadanda ke alamta shekarun gargajiyar kasar Sin, a don haka ana iya cewa, bana shekarar 2020 ta kasance wani sabon babi, ana sa ran Najeriya za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da kasar Sin bisa shawarar ziri daya da hanya daya domin tabbatar da matsayar da aka cimma yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, tare kuma da ciyar da huldar abokantaka tsakanin Sin da Najeriya gaba yadda ya kamata, kana yana fatan kasashen Najeriya da Sin za su samu sabon ci gaba tare a shekarar bera da muke ciki, har ma al'ummomin kasashen biyu za su kara jin dadin rayuwarsu.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China