Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na kara kokarin kare 'yancin mallakar fasaha
2020-01-22 19:33:58        cri

Yau a nan birnin Beijing kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana cewa, kasar Sin tana kara kokari matuka domin kare 'yancin mallakar fasaha, kana ya fayyace cewa, yanzu kasar Sin tana sanya kokari domin shiga yarjejeniyar Hague kan batun yin rajistar zanen siffar kayayyakin masana'antu.

Kwanan baya, jaridar Financial Times ta Birtaniya ta buga wani rahoto cewa, kasar Sin tana kokarin kare 'yancin mallakar fasaha, musamman ma ta fuskar kirkire-kirkire. Kan wannan, Geng Shuang ya bayyana yayin taron ganawa da manema labarai cewa, yanzu kasar Sin ta kai matsayi na biyu a duniya a fannin nazarin kimiyya da fasaha, adadin neman samun 'yancin mallakar fasaha a kasar Sin ya kai sahun gaba a duniya, kana adadin wadanda suka samu 'yancin mallakar fasahar ya kai matsayi na uku a duniya. Ban da haka rahoton mai taken "Alkaluman kirkire-kirkiren duniya na shekarar 2019" da kungiyar kare 'yancin mallakar fasahar duniya ta fitar ya nuna cewa, kasar Sin tana matsayi na 14 a fadin duniya, wato ta daga matsayinta a cikin shekaru hudu a jere da suka gabata.

Geng Shuang ya yi nuni da cewa, a matsayinta na kasar dake kan gaba a fannin kirkire-kirkire da kare 'yancin mallakar fasaha a duniya, kasar Sin za ta ci gaba da kara karfinta a bangaren kare 'yancin mallakar fasaha, ciki har da yin kirkire-kirkire da gudanar da harkokin dake shafar aikin da kuma samar da hidimar da ake bukata.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China