Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya tattauna da shugabannin Faransa da Jamus ta wayar tarho gabanin bikin bazara
2020-01-22 20:32:22        cri

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Faransa Emmanuel Macron da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta wayar tarho gabanin bikin bazara na sabuwar shekarar al'ummar Sinawa.

Yayin tattaunawar, shugabannin biyu sun mika sakon gaisuwar bikin bazarar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiuar kasar Sin ga shugaba Xi da daukacin al'ummar Sinawa, tare da yi musu fatan samun nasara da kasancewa cikin farin ciki.

A nasa bayanin, shugaba Xi ya mika sakon gaisuwar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ga jagororin kasashen biyu da al'ummominsu. Ya yi fatan cewa, Sin da Jamus za su kasance abokan dogara da juna da kara yin hadin gwiwa fiye da bambancen-bambance dake tsakaninsu. Xi ya yi kira ga takwaransa na Faransa da su kara zage damtse wajen bunkasa alakar dake tsakanin sassan biyu gami da musaya tsakanin manyan jami'an kasashen biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China