Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Li Keqiang ya yi kira da a kara azama wajen kyautata rayuwar al'umma
2020-01-23 10:39:40        cri
Firaminstan Sin Li Keqiang, ya yi kira ga sassan hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki, da su kara zage damtse wajen yin aiki tukuru, domin warware matsalolin dake addabar al'ummar kasar Sin, tare da aiwatar da matakan kara kyautata rayuwar daukacin kabilun kasar bisa dabarun samar da ci gaba.

Li, wanda kuma mamba ne a ofishin zaunannen kwamitin siyasa na kwamitin kolin jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya yi wannan kira ne, yayin da ya ziyarci lardin Qinghai dake arewa maso yammacin Sin a ranekun Talata da Laraba.

A wani kauye da ya ziyarta mai kunshe da kabilun Han da Tibet, firaministan ya duba yanayin rayuwar al'umma, tare da gabatar musu da sakon sabuwar shekara. Ya ce akwai bukatar yankin yammacin kasar ya bunkasa sabon tsarin zamanantar da birane, ya kuma samar da damar karin ci gaba ga biranen, ta yadda hakan zai fadada guraben ayyukan yi ga manoma, har su kai ga fita daga kangin talauci.

Daga nan sai ya bukaci samar da tsarin hadin gwiwar gwamnati da mazauna yankin, domin cimma nasarar gyara gidajen dake unguwannin yankin, da kyautata tsarin kula da tsofaffi, da na kiwon lafiya, da tsaftar muhalli, da kara kyautata rayuwar al'umma, musamman ma yara kanana da wadanda suka manyanta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China