Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin intanet na kasar Sin sun samu bunkasar kudaden shiga a shekarar 2019
2020-01-23 11:51:51        cri
Kamfanonin intanet na kasar Sin da sauran bangarorin ba da hidima masu alaka da su sun samu gagarumin ci gaba wajen bunkasuwar samun kudaden shiga a shekarar 2019 kasancewar sabbin fasahohi da wasu manhajoji sun kara taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsayin tattalin arzikin kasar.

Wadannan kamfanonin, kowanensu ya samar da kudin shiga a shekara na sama da yuan miliyan 5 kwatankwacin dala 724,400 a shekarar 2018, baki daya sun samar da kusan RMB yuan tiriliyan 1.21 a bara, inda ya karu da kashi 21.4 bisa 100, idan an kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2018, kamar yadda wasu alkaluman da ma'aikatar kula da masana'antu da fasahar sadarwa ta zamani ta kasar Sin (MIIT) ta bayyana.

Ribar da masana'antu suka samar ya karu da kashi 16.9 bisa 100 idan an kwatanta da makamancin lokacin 2018, wanda ya kama kashi 13.1 bisa 100.

Kudaden da aka kashe wajen bincike da raya ci gaba ya zarta na kudaden shigar, inda ya karu da kashi 23.1 bisa 100, kamar yadda alkaluman na MIIT suka nuna. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China