Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
ILO: Hadin gwiwar kasa da kasa yana da muhimmanci wajen tunkarar duk wata barazana
2020-01-23 11:58:17        cri
Darakta janar na hukumar kwadago ta kasa da kasa (ILO), Guy Ryder, ya bayyana cewa hadin gwiwar kasa da kasa da dunkulewar hukumomin bangarori daban daban babban muhimmin mataki ne da zai taimaka wajen tunkarar manyan kalubalolin dake yiwa duniya barazana.

A wata hirar da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, a yayin halartar taron dandalin tattalin arzikin kasa da kasa na Davos karo na 50, Ryder ya ce, a halin yanzu akwai manyan al'amurra dake damun duniya kamar matsalolin sauyin yanayi, rashin daidaito, bakin haure, kuma matsaloli ne da kasa guda daya ba za ta iya magance su ita kadai ba.

Ya ce wadannan batutuwa za'a iya magance su ne ta hanayar hadin gwiwar bangarori daban daban.

Ryder ya yabawa kasar Sin bisa ga goyon bayan da take baiwa ra'ayin hadin gwiwar bangarori daban daban, wanda a halin yanzu tsarin ke fuskantar matsin lamba, kana ya kara da cewa, za su ci gaba da neman gwamnatocin kasashe kamar gwamnatin Sin da su ci gaba da bada gudunmowa wajen cimma wannan buri. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China