Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi ya jaddada bukatar zage damtse don cimma burin farfado da kasa
2020-01-23 19:59:49        cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya bukaci daukacin Sinawa, da su kara zage damtse don ganin sun cimma nasarar mafarkinsu na farfado da kasa, domin a cewarsa, lokaci da tarihi duk ba sa jiran kowa, kasancewar dukkansu na tare da masu aiki tukuru.

Xi, wanda har ila shi ne babban sakataren kwamitin koli na JKS kana shugaban kwamitin koli na rundunar sojojin kasar, ya bayyana haka ne, yayin da yake jawabi Alhamis din nan a liyafar murnar bikin sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin da aka shirya a babban dakin taron jama'a dake birnin Bejing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya ce, karkashin jagorancin JKS, wajibi ne dukkan mambobin jam'iyya da rundunar sojojin kasar da dukkan 'yan kabilu daban-daban su tsaya tsayin daka, su tunkari kalubale da kama turbar cimma manufofin farfado da kasa da aka sanya a gaba da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China