Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a gabatar da fim din bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin a sinima
2020-01-23 22:17:25        cri

Karon farko ne za'a gabatar da fim din bikin kade-kade da raye-raye na murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiya ta kasar Sin na bana da babban gidan rediyo da talabijin na kasar wato CMG zai shirya a sinima. A yau Alhamis ne, an yi taron manema labarai kan fim din bikin a Beijing, wanda ya samu halartar shugaban CMG Shen Haixiong da wasu jami'an kwamitin kula da harkokin kabilu na kasar Sin.

Za a fassara fim din zuwa yaren Guangdong, da na Minnan, da na Chaoshan da kuma na Kejia, har da harsunan kananan kalibun kasar Sin guda biyar, ciki har da harshen Mongolia, da na Tibet, da na Uygur, da na Kazak da ma na Koriya, domin al'ummar Sin da ke wurare daban daban da kabilu daban daban za su iya jin dadin kallon shirye-shiryen bikin bazara da CMG zai gabatar. Ban da wannan kuma, za a fassara fim din zuwa wasu harsunan kasashen waje da ma watsa su a talibijin da sinama da ke kasashen.

Za a yi amfani da wasu fasahohin zamani kamar 4K wajen daukar hoton bidiyon shirye-shiryen, sa'an nan za a yi edita kansu da ma kyautata hotunan bidiyon, domin biyan bukatun masu kallon fim.(Murtala, Kande)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China