Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta ba da rahoton kamuwar mutane 830 da cutar nan ta numfashi
2020-01-24 14:47:16        cri
Hukumomin lafiya a kasar Sin sun sanar a Jumma'ar nan cewa, ya zuwa jiya Alhamis, an tabbatar da cewa, mutane 830 sun kamu da cutar nan ta numfashi wadda kwayar cutar coronavirus (2019-nCov) ke haddasawa a yankuna 29 na lardunan kasar.

Hukumar lafiya ta kasar ta bayyana cewa, daga cikin wannan adadi, mutane 34 sun warke har an sallame su daga asibitoci daban-daban da aka kwantar da su. Mutane 1,072 ne dai aka yi zaton sun kamu da cutar a yankuna 20 na lardunan kasar.

Ya zuwa yanzu, cutar ta halaka mutane 25, ciki har da mutane 24 a lardin Hubei dake tsakiyar kasar Sin, da mutum guda a lardin Hebei dake arewacin kasar.

Sai dai kuma ya zuwa tsakar daren jiya Alhamis, an ba da rahoton kamuwar mutane biyar, wato mutum biyu a yankin Hong Kong, biyu a Macao, sai mutum guda a yankin Taiwan.

A kasashen ketare kuma, an tabbatar da kamuwar mutane uku a Thailand, inda mutum biyu daga cikinsu suka warke. An kuma tabbatar mutum guda da ya kamu da cutar a Japan ya warke. Haka kuma an tabbatar da kamuwar mutane daddaya a kasashen Koriya ta kudu da Amurka da Singapore, sai mutane biyu a kasar Vietnam.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China