Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bikin bazara na bana na da ma'ana ta musamman
2020-01-24 16:17:36        cri

Yau Juma'a, jajebirin sabuwar shekara ce bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma muhimmiyar rana da Sinawa ke haduwa da iyalansu. Amma, sakamakon bullar sabuwar cutar numfashi wadda kwayoyin cutar "coronavirus" ke haddasawa, Sinawa da yawa sun bar damar haduwa da iyalansu kamar yadda aka saba, ko saboda kokarin yaki da cutar, ko suna kebe kansu don hana yaduwar cutar, har ma da soke shirye-shiryensu na yawon shakatawa don kiyaye lafiyar sauran mutane.

Abun da ya fi burge wa shi ne, masu aikin jinya na yankuna daban daban na kasar Sin sun tafi birnin Wuhan, don hada kai tare da takwarorinsu na birnin wajen yaki da cutar, wadanda suka nuna tunaninsu na sadaukar da ayyukansu, da kwarewarsu.

Dukkan abubuwan da muka bayyana a baya, suna da nasaba da matakai masu dacewa da gwamnatin kasar Sin ta dauka, da hadin kai da ta yi tare da kasa da kasa. A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, gwamnati ta saka sabuwar cutar numfashi wadda kwayoyin cutar "coronavirus" ke haddasawa cikin cututtuka masu yaduwa da ake kulawa da su bisa tsarin doka, an kuma rufe hanyoyin shiga da fita a birnin Wuhan na dan wani lokaci, baya ga haka, an samar da tallafin kudi na RMB biliyan 1 cikin gaggawa don tinkarar cutar, duk matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka sun nuna cewa, gwamnatin kasar na dora muhimmanci kan jama'arta, tana kuma ba da muhimmanci ga batun da ya shafi kiwon lafiyar jama'a.

Yanzu Sinawa biliyan 1.4 na hada kai, don yaki da cutar ta numfashi. Don haka, bikin bazara na wannan shekara na da ma'anar musamman ta kishin kasa da kaunar jama'a ga al'ummar Sinawa. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China