Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Dandalin cinikayya ta intanet na Jumia na sa ran kara habaka bisa kwarin gwiwar da yake samu daga Kasar Sin
2020-01-25 16:25:08        cri
Dandalin cinikayya ta intanet na nahiyar Afrika wato Jumia, na samun kwarin gwiwa daga kamfanonin cinikayya ta intanet na kasar Sin, inda ya ke sa ran koyi da su a wannan fannin a nahiyar Afrika.

Jeremy Hodora, daya daga cikin wadanda suka kafa katafaren dandalin ne ya bayyana haka a jiya, jim kadan bayan Kamfanin ya sanar da nada sabon shugaba a Nijeriya.

Jeremy Hodara, ya bayyanawa Xinhua cewa, Kasar Sin ta ci gaba a fannin fasaha, musammam wajen amfani da tsarukan cinikayya da biyan kudi ta intanet.

Ya ce, kamfanonin fasahar sadarwa da na cinikayya ta intanet suna da kyakkywar fahimta game da yadda cinikayya ta intanet take, kuma kasar Sin na da yanayin muhalli dake kama da na nahiyar Afrika fiye da Amurka da Turai, wanda ya ce ya ba su kwarin gwiwa, kuma suna bin wannan alkiblar domin su ci gaba da yin tasiri a nahiyar Afrika.

Ya kara da cewa, kamfaninsu na iya koyon darrusa masu muhimmanci daga kamfanonin fasaha na Sin, musammam katafaren kamfanin Alibaba.

Har ila yau, ya shaidawa Xinhua cewa, Jumia na mayar da hankali kan tsarin cinikayya da zai dace da nahiyar tare da jajircewa wajen yin kasuwanci bisa la'akari da muradunta. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China