2020-01-25 16:48:18 cri |
Stephen Njoka, Darakta Janar na hukumar yaki da kwari ta gabashin Afrika, ya ce kwarin da aka samu rahoton ganinsu a arewacin Kenya a watan Disamban bara, na tunkarar yankunan Baringo da Turkana na kudu maso yammacin Kenya.
Ya ce hadarin bazuwarsu zuwa kasashen 3 na da karfi sosai, la'akari da karancin ayyukan yaki su a wasu kasashen, da kuma yadda suke da karfin tafiya da hayayyafa.
Jami'in ya ce, hukumar da abokan huldarta a shirye suke, kana suna da isassun magungunan feshin kwari da jiragen domin yaki da kwarin masu saurin tafiya.
A nasa bangaren, mataimakin Darakta Janar na hukumar samar da abinci da kula da aikin gona na MDD, kuma wakilin hukumar a nahiyar Afrika, Bukar Tijjani, ya ce shigowar kwarin na barazana ga wadatar abinci da rayuwar jama'a a yankin gabashin Afrika. (Fa'iza Mustapha)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China