Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An samu mutum guda da ya kamu da cutar zazzabin Lassa a arewacin Najeriya
2020-01-26 15:47:53        cri
Hukumomi sun tabbatar da cewa an samu rahoton mutum guda da ya kamu da cutar zazzabin Lassa a yankin Chikun dake jahar Kaduna a arewacin Najeriya.

Kwamishiniyar lafiya ta jahar Kaduna Amina Mohammad Baloni ta bayyana cikin wata sanarwa cewa wani mutum dan shekaru 36 da haihuwa yana karbar magani a cibiyar yaki da cutar da aka kebe ga wadanda suka kamu da cutar.

Ta baiwa mazauna yankunan tabbaci cewa gwamnati ta yi kyakkyawan tanadin kayayyakin kiwon lafiya a dukkan asibitocin dake kasar, kana ana cigaba da ankarar da jama'a game da illolin cutar.

Baloni ta kuma bukaci mazauna yankin da su maida hankali wajen tsabatace muhallinsu don gudun yaduwar cutuka.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China