Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD ta yi Allah wadai da karya dokar takunkumin hana yaduwar makamai a Libya
2020-01-26 16:36:46        cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a kasar Libya (UNSMIL), a jiya Asabar ya bayyana rashin jin dadi bisa yadda ake cigaba da karya dokar takunkumin hana yaduwar makamai a kasar Libya, yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin sojoji dake da sansani a gabashin kasar da kuma bangaren sojojin gwamnati dake samun goyon bayan MDD.

A ranar 19 ga watan Janairu, mahalarta taron zaman lafiya na birnin Berlin sun amince zasu mutunta dokar takunkumin hana yaduwar makamai a Libya wanda kwamitin sulhun MDD ya amince da ita.

Sai dai an ga wasu manyan jiragen saman dakon kaya da wasu jiragen sama sun sauka a filayen jiragen sama dake gabashi da yammacin Libya a 'yan kwanakin da suka gabata, inda suka sauke manyan makamai, da tankokin yaki, da masu bada shawara da kuma mayaka na bangarorin biyu, a cewar sanarwar.

Shirin MDD yayi Allah wadai da yadda ake cigaba da saba yarjejeniyar, lamarin da zai iya jefa kasar cikin sabon tashin hankali da barkewar yaki.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China