Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da bikin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a Najeriya
2020-01-26 16:37:14        cri
Dandazon mahalarta kasaitaccen bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa bisa kalandar gargajiyar kasar Sin ta shekarar 2020 sun nishadantu da wasannin gargajiya nau'i daban daban wanda aka gudanar a ranar Asabar a Abuja, babban birnin Najeriya.

Daga cikin mahalarta bikin, akwai jami'an diflomasiyya, manyan jami'an gwamnati, da shugabannin kamfanoni, inda suka nuna gamsuwarsu game da bikin wanda ya hada da kide kide da raye raye da sauran wasannin gargajiya, wanda kuma aka gudanar don murnar sabuwar shekarar bisa kalandar gadajiyar kasar Sin ta wannan shekarar a Abuja.

Al'ummar Sinawa mazauna Najeriya sun gudanar da shagulgulan gargajiyar wanda ya samu halartar al'ummomin kasashen biyu, har ma da jama'ar wasu kasashen duniya, wadanda suka zo daga wuraren na kusa da na nesa domin samun karin fahimta dangane da al'adun kasar Sin da kuma kallon kayatattun wasannin gargajiyar kasar Sin da aka nuna yayin bikin.

Bikin, wanda ofishin jakadancin kasar Sin a Najeriya tare da hadin gwiwar cibiyar raya al'adun kasar Sin dake Abuja suka shirya, ya samu dubun mahalarta, ciki har da daliban manyan makarantu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China