Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Algeria tace Mali zata yi galaba a yaki da ta'addanci
2020-01-27 17:27:55        cri
Kasar Algeria ta yi Allah wadai da babbar murya game da harin ta'addanci da aka kaddamar a sansanin sojoji na Sokolo dake tsakiyar kasar Mali.

Abdelaziz Benali Cherif, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Algeria ya fada cikin wata sanarwar da aka baiwa kamfanin dillancin labarai na APS cewa, kasar Algeriya tana da kwarin gwiwar Mali ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen yakar ayyukan ta'addanci.

Cherif yace, kasarsa tayi matukar jinjinawa sadaukar da kan da sojojin Mali suka nuna wadanda suka mutu a bakin daga domin aikin kare kasarsu da kuma al'ummar kasar.

Kimanin sojoji 19 aka hallaka tare da wasu 5 da suka jikkata a safiyar ranar Lahadi a wani harin ta'addanci da aka kaddamar kan sansanin sojojin dake tsakiyar Mali, kamar yadda kafafen yada labaran cikin gidan kasar suka bayar da sanarwa daga rundunar sojojin kasar Mali.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China