Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD tayi Allah wadai da harin da aka kaddamar a filin jirgin saman Tripoli na kasar Libya
2020-01-27 17:28:51        cri
Shirin bayar da tallafi na MDD a kasar Libya (UNSMIL), yayi Allah wadai da harin da aka kaddamar a filin jirgin saman Mitiga dake Tripoli babban birnin kasar Libya, yayin da ake cigaba da gwabza yaki tsakanin sojojin dake da sansani a gabashin kasar da kuma sojojin dake samun goyon bayan MDD.

A sanarwar da UNSMIL ya wallafa a shafinsa na twitter, yayi Allah wadai da babbar murya game da harin da aka kaddamar a filin jirgin saman na Mitiga, wanda aka harba makamai masu linzami biyu, lamarin da yayi sanadiyyar raunata fararen hula biyu, kana ya lalata titin filin jirgin saman da wasu gine gine.

UNMSIL ya jaddada cewa, harin da aka kaddamar kan fararen hula, musamman gine gine gwamnati, ya sabawa dokokin jin kai na kasa da kasa, kana cigaba da kaddamar da hare haren kan filin jirgin saman na Mitiga ya take hakkin al'ummomi miliyan biyu dake zaune a babban birnin kasar wajen hana su amfani da filin jirgin saman yadda ya kamata.

Dakarun sojojin gwamnati dake samun goyon bayan MDD sun ce sojojin dake da sansani a gabashin kasar ne suka kaddamar da harin filin jirgin saman kasar.

A ranar Larabar da ta gabata ne sojojin masu sansani a gabashin kasar suka ayyana farfado da wani shirin kaddamar da hari da zummar hana tashin jirgin sama a yammacin Libya, inda a can ne filin jirgin saman Mitiga na kasa da kasa yake.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China