Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 14 sun mutu a wani harin 'yan bingida a shiyyar tsakiyar Najeriya
2020-01-28 16:20:43        cri
Kimanin mutane 14 ne 'yan bindiga suka hallaka a wani kauyen jahar Plateau dake shiyyar tsakiyar Najeriya, wasu majiyoyi daga yankin sun bayyana faruwar lamarin.

Akwai wasu mata biyu daga cikin wadanda harin ya rutsa dasu a kauyen Kwatas dake karamar hukumar Bokkos a jahar da yammacin ranar Lahadi, wani jami'in hukumar tsaron sakai na yankin ya bayyana faruwar lamarin.

Titus Ayuba, tsohon dan majalisar dokokin jahar ya ce, maharan sun afkawa kauyen.

Ayuba yace 'yan bindigar sun kaddamar da harin ne a kasuwar kauyen inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi.

Abu Gabriel, kakakin hukumar 'yan sandan jahar, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua faruwar lamarin sai dai bai bayyana hakikanin mutanen da lamarin ya rutsa dasu ba.

Augustine Agundi, kakakin rundunar tsaron musamman na jahar, ya shedawa Xinhua cewa, an tura jami'an tsaro zuwa yankin, domin dakile cigaba da kaiwa hare haren.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China