Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakile wasu hare haren mayakan Boko Haram
2020-01-28 16:36:37        cri
Wata sanarwa da rundunar sojojin Najeriya ta fitar, ta ce dakarun ta sun dakile wasu hare haren mayakan Boko Haram, a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Da yake tabbatar da hakan, kakakin rundunar Aminu Iliyasu, ya ce sojoji na ci gaba da dakile harin mayakan, ciki hadda na ranar 18 ga watan nan, wanda 'yan Boko Haram din suka yi yunkurin kaiwa Gamborou-Ngala.

Ya ce mayakan sun kutsa yankin ne, cikin wasu motoci 5 da suka daurawa bindigogi, wasu kuma a kan babura, suna buya cikin gonakin yankin. Iliyasu ya ce sun yi nufin aukawa mazauna Gamborou-Ngala, kafin dakarun sa kai dake tallafawa sojoji su gano su, wanda hakan ya haifar da musayar wuta, kuma nan take 'yan ta'addan suka tsere.

Ya ce binciken farko ya nuna cewa, 'yan ta'addan dake tare da 'yan kunar bakin wake, sun yi nufin tarwatsa sansanin 'yan gudun hijira ne dake Gamborou-Ngala.

Rahotanni sun nuna cewa, an ceto wasu jami'an ba da agaji su 5, da suka buya cikin wani ramin karkashin kasa, yayin musayar wuta da sassan biyu suka yi. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China