Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban rukunin likitoci na Sin dake kasar Namibia Chu Hailin wanda ke samar da gudummawa a Namibia
2020-02-03 14:07:00        cri

A lokacin hutun bikin bazara na kasar Sin, akwai wasu Sinawa da suka gudanar da ayyukansu a kasashen waje, wadanda ba su iya komawa gida don zama tare da iyalai a lokacin ba. Cikin su akwai ma'aikata masu gudanar da manyan ayyuka, da masu aikin hada-hadar kudi, da likitocin da suke bada jinya a kasashen waje, da malamai masu koyar da Sinanci da sauransu, dukkansu sun gudunar da ayyuka don sada zumunta a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya. Ga wani likita da ya samar da gudummawa a kasar Namibia mai suna Chu Hailin.

A kasar Namibia dake kudu maso yammacin nahiyar Afirka, wani likita mai fasahar jinya ta gargajiya na Sin, ya jagoranci wani rukunin likitoci da gudanar da aikin jinya ta gargajiya na Sin a kasar, kuma wannan ne rukunin likitoci mafi kankanta da Sin ta tura zuwa kasashen waje, wanda ya samu goyon baya da yabo daga jama'ar kasar Namibia, kana an yada al'adun fasahar jinya ta gargajiya ta Sin a kasar.

Da karfe 8 na safiya, Mr Kristof dake zaune a yankin Ondangwa na arewacin kasar Namibia, ya yi tafiya ta tsawon kilomita fiye da 600, zuwa cibiyar bada jinyar gargajiya ta kasar Sin dake asibitin Katutura, kuma shugaban rukunin likitoci na kasar Sin dake kasar karo na 12 Chu Hailin ya karbe shi.

Ya yi bincike kan Mr Kristof, da shirya gadon jinya gare shi, da yin allurar gargajiya gare shi. Chu Hailin ya bada jinya ga mutane da dama. Chu ya bayyana cewa,  

"Mutane da dama sun zo sun ga likita, muna iya bada jinya ga mutane 121 a duk rana. Muna da likitoci biyu da ma'aikatan jinya biyu, amma muna da gadoji 9 ne kacal. Muna yin amfani da dukkan kayayyaki don kara bada jinya ga mutane."

Tun daga shekarar 1996, rukunin likitoci na Sin dake kasar Namibia ya kiyaye bada jinya a asibitin Katutura, kwamitin kula da kiwon lafiya na lardin Zhejiang ya tura rukunin, wanda ya hada da likitoci biyu da ma'aikatan jinya biyu, an kan kira shi da rukunin likitoci mafi karami na Sin da aka tura shi zuwa kasashen waje. Koda yake likitoci da ma'aikata dukkansu hudu ne kacal, amma sun gudanar da ayyuka da dama. Tun daga ranar 2 ga watan Yuni na shekarar 2018 zuwa ranar 31 ga watan Disamba na shekarar 2019, rukunin likitoci na Sin dake kasar Namibia karo na 12 da Chu Hailin ya jagoranta, ya karbi, da bada jinya ga mutane 22,509. A kan samu mutane da dama da suka zo cibiyar bada jinyar gargajiya ta kasar Sin, dake asibitin Katutura a kowace rana, kana babu wanda ya nuna rashin jin dadi ga cibiyar.

Chu Hailin mai shekaru 52 da haihuwa a bana ya zo kasar Namibia sau uku, wanda ya taba zuwa kasar sau biyu tun daga shekarar 2008 zuwa 2012. Kana ya samu lambar yabo ta likita mafi kyau na kasar Sin da ya gudanar da ayyukan jinya a kasashen waje a shekarar 2013. A shekarar 2018, Chu Hailin ya sake zuwa kasar Namibia, ya kara sanin alhakinsa a matsayin likita mai bada jinya a kasashen waje, ya ce,

"Yawan mutanen da muka duba a nan ya fi na cikin kasar Sin, hakan ya shaida cewa, fasahar jinya ta gargajiya ta Sin tana da amfani. Muna wakiltar kasarmu da gudanar da ayyuka, wannan tunani ya sa kaimi gare mu na zuwa nan. A matsayin mu na likitoci, mun bada jinya da samar da hidima ba tare da biyan kudi ba. Muna samu yabo, kana hakan ya daga mutuncin kasarmu sosai."

Chu Hailin da abokan aikinsa sun yi kokarin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, sun samu yabo da suna a dukkan kasar Namibia. Mutanen da suka taba samun jinyar allurar gargajiya ta Sin da rukunin ya yi musu sun hada da shugaban kasar Namibia, da fararen hula da dama, dukkansu sun nuna yabo ga rukunin. Mr Constantin wanda ya samu jinyar allurar gargajiya ta Sin sau biyar ya bayyana cewa,

"Allurar gargajiya ta Sin tana da amfani sosai. Ina jin gamsuwa sosai, shawarar da na bayar ita ce, a yada wannan fasahar jinya, ta haka karin mutanen kasar Namibia za su samu irin wannan jinya. Lokacin da na zo nan da farko, ina tafiya ne da sanda, a gani na ba zan iya sake tafiya ba. Yanzu na samu sauki sosai. Ina jin wannan fasahar jinya tana da amfani sosai." (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China