Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan Nijeriya dake kasar Sin suna karfafa al'ummar Sinawa kwarin gwiwar yaki da cutar numfashi
2020-02-04 11:41:17        cri

 


Al'ummar Sinawa a yanzu haka na hada hannu don yin iyakacin kokarin yaki da cutar numfashi da kwayar cutar Novel Coronavirus ke haddasawa, a daidai wannan lokaci, jerin wasu hotunan da aka hada masu taken "Karawa Wuhan kwarin gwiwa da fatan alheri ga kasar Sin" sun samu karbuwa tsakanin 'yan Nijeriya mazauna kasar Sin. Wadansu sun saka hotunan a matsayin alamarsu ta kafar sada zumunta ta Wechat don nuna goyon baya ga Wuhan da karawa kasar Sin kwarin gwiwa.

Kungiyar 'yan Nijeriya mazauna kasashen waje reshen kasar Sin ce ta hada tare da gabatar da wadannan hotuna, inda aka yi amfani da launin ja tare da yin ado da fitilu da kullin nuna fatan alheri na kasar Sin da alamun tutocin kasashen biyu, da dai sauran abubuwa, sannan kuma aka rubuta kalmomi "Karawa Wuhan kwarin gwiwa" da "fatan alheri ga kasar Sin", da kuma "Muna tare da Sinawa a wannan mawuyacin hali", da "Ba shakka za mu daidaita wannan matsala cikin hadin kai" da sauransu cikin Turanci da kuma Sinanci.

Wani jami'in gudanarwa na kungiyar Louis Idehen ya ce, an tsara da gabatar da wadannan hotuna ne don bayyana goyon baya ga wannan kasa mai martaba, musamman ma don karfafa wa jama'ar Wuhan kwarin gwiwa, kuma suna tsayawa ga goyon bayan jama'ar kasar Sin da ba da taimako gwargwadon karfinsu, don cimma nasarar yaki da cutar tun da wuri. Ya ce, suna karfafa wa kasar Sin da Wuhan kwarin gwiwa.

Ibrahim Aliyu mai karatun digiri na biyu a jami'ar nazarin aikin likitanci na garin Jinzhou da ke lardin Liaoning na kasar Sin ya saka wani hoton a kafar Weichat, kuma a game da dalilin da ya sa hakan ya ce:

"Kasar Sin kamar ni shi ne gidana na biyu, ko in ce shi ne gidanmu na biyu, ta bamu abun da kasarmu ce kawai za ta iya ba mu, sannan ba abun da za mu ce da kasar Sin sai godiya. To, kasar Sin da kuma mutanen da suke cikin kasar Sin, musamman mutanen Wuhan, muna so mu fada musu muna tare da su, kuma muna musu addu'a, in shaa Allahu muna ganin, in shaa Allahu wannan abu ya kusa ya kawo karshe, za su iya yakar wannan cuta."

Ibrahim Aliyu ya kuma jinjinawa gwamnatin kasar Sin bisa matakai masu inganci da ta dauka na yaki da cutar, ya ce, Sin na yin iyakacin kokarinta don hana yaduwar cutar. Ya kara da cewa, ya taba ziyartar Wuhan sau biyu, a ganinsa, birni ne mai kyau, kuma ya yi imanin cewa, Wuhan zai farfado karkashin kokarin gwamnatin Sin da jama'arsa.

Shi ma Yahaya Babs, wani dan Nijeriya da ke aiki a nan birnin Beijing, ya saka hoton karawa Wuhan kwarin gwiwa a matsayin alamarsa ta Weichat. Inda ya ce:

"Da farko dai, mu 'yan Nijeriya ne, kasarmu ta haihuwa. To Allah ya kaddara muna zaune a nan kasar Sin, da mu da mutanen Sin mun zama abu daya a namu fahimtar, walau aiki muke anan, walau karatu muke, a yanzu haka a kasar Sin muke. To idan abu ya samu dan uwanka a namu fahimtar, ya kamata ka nuna damuwarka ka nuna kana tare da shi. 'Yan Nijeriya mazauna kasar Sin, suma suna tare da mutanen Sin a cikin wannan hali da ake ciki, shi yasa muka kirkiri wannan hoton na "Jia You". Mutanen Sin, Sinawa muna tare da ku. Mu mutanen Nijeriya mazauna kasar Sin. Wato wannan nuna jajenmu ne da nuna jinjina ga jajircewa da gwamnatin kasar Sin ta yi, da juriya kuma da mutanen Wuhan musammam inda wannan cuta ta barke, to ta hakan ne muke nuna namu goyon baya, cewar muna tare da su a duka halin da ake ciki. "

Babs ya ce, Iyalai da kuma abokansa a gidan Nijeriya na buga masa waya don jin halin da yake ciki a kwanakin baya-baya nan, kuma ya kan amsa cewa, yana cikin koshin lafiya. Gwamnatin Sin na daukar ingantattun matakan da suka dace don hana yaduwar cutar, musamman ma yadda ta kwashe kimanin kwanaki 10 ta gina asibitoci biyu a Wuhan cikin gaggawa, abin da ya burge shi matuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China