Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Asibitin Huoshenshan ya karbi jerin farko na masu cutar numfashi
2020-02-05 14:53:44        cri

Da safiyar Jiya Talata, wasu motocin daukar marasa lafiya 10, suka kwashe wasu masu cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haifarwa, daga asibitocin da ke kula da su, zuwa asibitin Huoshenshan, da a kwanan nan aka kammala ginawa a birnin Wuhan, musamman domin kula da masu cutar.

Kawo yanzu dai, asibitin Huoshenshan ya karbi jimilar mutane 45 masu fama da cutar numfashi da kwayar cutar corona ke haddasawa. Sabili da yadda aka gina asibitin cikin gaggawa, har yanzu akwai wasu dakunan asibitin da ake dubawa don tabbatar da ko sun cancanci karbar masu cutar. An yi hasashen nan da wasu kwanaki uku zuwa biyar, za a fara aiki da dakunan baki daya. Ban da wannan, ana kuma kokarin gina wasu asibitoci uku a birnin Wuhan, wadanda ake sa ran za su iya samar da gadaje kimanin 3400 idan aka kammala su.

Mr. Xu Dixiong, mataimakin shugaban asibitin Huoshenshan, ya ce, an tura ma'aikatan lafiya kimanin 1,400 daga rundunonin soja zuwa asibitin, musamman domin kula da masu cutar. Masu cutar 45 da aka karba a jiya Talata, dukkansu ba su cikin yanayi mai tsanani.

Bayan an gyaggyara tare da inganta dakunan asibitin cikin kwanaki masu zuwa, ma'aikatan lafiya za su fara karbar sauran masu cutar, sannan za a kuma ware isassun likitoci ga masu cutar da suka yi tsanani.

Rahotanni na cewa, mahukuntan birnin Wuhan na daukar matakai domin daidaita matsalar karancin samun gadajen asibiti ga masu cutar. Malam Jiang Rongmeng, likitan asibitin Ditan na birnin Beijing, wanda kuma ke cikin rukunin masana ta hukumar lafiya ta kasar Sin, ya bayyana cewa, yanzu haka ana kokarin gina wasu asibitocin wucin gadi guda uku a cibiyar baje kolin kasa da kasa da ke birnin Wuhan da filin wasanni na Hongshan da sauransu, domin karbar masu cutar da ba su yi tsanani ba. Bayan an kammala asibitocin, ana sa ran za su samar da gadaje 3400, kuma ya zuwa lokacin, asibitocin birnin Wuhan za su tura likitocinsu zuwa wuraren, domin su kula da masu cutar. Mr. Jiang Rongmeng ya kara da cewa, "An gina asibitocin musamman domin a kebe masu cutar wadanda ba su yi tsanani ba, bisa la'akari da yanayin lafiyarsu kuma, za a kai wadanda suka fara yin tsanani zuwa sassan da aka ware musamman domin wadanda yanayinsu ya yi tsanani. Za kuma a sallami wadanda suka warke daga cikin wadanda ba su yi tsanani ba, idan sun cancanci hakan. Idan aka fara aiki da wannan tsari, za a kai ga rage lokacin samar da gadaje ga masu cutar."

Dongane da matsalar karancin samun kayayyakin gwajin kwayoyin cutar, Malam Jiang Rongmeng ya ce, kawo yanzu, an sayi kayayyakin gwajin da suka kai dubu 100, a sa'i daya kuma, wasu asibitoci na birnin Wuhan sun rage lokacin da suke bukata wajen gudanar da gwaji, wato daga kwanaki uku ko hudu zuwa kwana daya tak, inda yanzu haka a cikin kwana daya za a iya tabbatar da ko an kamu da cutar ko a'a. Ya kuma kara da cewa, wasu asibitoci a birnin Wuhan suna iya gudanar da gwajin kwayoyin cutar da kansu, hakan ya rage lokacin da ake batawa wajen kai samfuran gwaji sassan da ake iya gudanar da gwajin tare da kara ingancin aikin. Ya ce, "Wadannan asibitoci suna iya gudanar da gwajin kwayoyin cutar da kansu, wato ba lalle su kai samfuran cibiyoyin dakile cutar ko wani bangare da ke iya samar da hidimar gwajin ba. Ta hanyar ware asibitocin da suke iya gudanar da gwajin a sassa daban daban na birnin Wuhan, za a iya kara ingancin gudanar da ayyukan gwaji."(Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China