Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatan kamfanin jiragen kasa na Kenya sun ba da gudunmawar yaki da cutar numfashi
2020-02-07 11:20:25        cri

Ma'aikatan kamfanin gudanar da harkokin jiragen kasa tsakanin Mombasa da Nairobi na kasar Kenya, sun ba da gudunmawar yaki da cutar numfashi don karawa kasar Sin kwarin gwiwa, daga cikin ma'aikatan dai, akwai Sinawa, da kuma 'yan kasar Kenya 180.

Jirgin kasa tsakanin Mombasa da Nairobi, aiki ne da ya zama abin koyi ga sauran sassa cikin shawarar "Ziri daya da hanya daya", kuma ya kasance layin dogo irin sa na farko da aka gina bisa fasaha da kimiyya na zamani a cikin shekaru dari da suka gabata a Kenya, inda ma'aikatan Sinawa da 'yan kasar Kenya kimanin 3000 suke kula da harkokin gudanar da shi.

Bisa ganin yadda kasar Sin na kokarin tinkarar cutar numfashi, kamfanin ya gudanar da aikin ba da kyautar kudi mai taken "Yaki da cutar cikin hadin kai". Sinawa masu aiki a kamfanin ne suka yi niyar yin wannan aiki na ba da gudunmawar su, amma sai ma'aikatan kamfanin 'yan kasar Kenya su ma suka nuna bukatar su ta ba da gudunmawarsu.

Mataimakiyar ministan sufurin fasinja na kamfanin, Madam Dinah Waithira Kimani, ta ba da kudin kasar Kenya shilling 5000. Tana mai cewa, ta taba ziyartar birnin Wuhan lokacin da take samun horo a kasar Sin. Yanzu kuma halin da birnin Wuhan ke ciki na fama da wannan cuta, ya taba zuciyarta kwarai. Ta ce, ta ji tausayi sosai kan mutane, da kuma iyalansu wadanda cutar ta ritsa da su. Hakan ya sa, ta ga ya dace ta ba da gudunmawarta don tinkarar wannan cutar.

Wuhan, birnin ne da ma'aikata 'yan kasar Kenya ba za su iya mantawa da shi ba, saboda sau da dama suna ziyarar sa, don samun horo. Mataimakin manajan kamfanin gudanarwa na Sammy Gachuhi na matukar kaunar birnin, ya kuma ba da kyautar kudin Kenya shilling 20000. Kuma ya yi imanin cewa, Sin za ta cimma nasarar wannan yaki, saboda ganin matakan da suka dace da gwamnatin kasar Sin ke dauka. Ya kara da cewa, matakan da gwamnatin Sin ke dauka na karawa mutane kwarin gwiwa, musamman ma asibitin da ta kafa cikin kwanaki 10 kacal. Babu shakka, Sin za ta shawo kan wannan cuta cikin gajeren lokaci, kana zaman rayuwar jama'a zai dawo yadda aka saba ba da jimawa ba.

Sakamakon barkewar cutar a kasar Sin, wasu 'yan Kenya na nuna bambancin ra'ayi, da rashin fahimta ga Sinawa. Game da hakan, mataimakiyar shugaban rukunin motocin sufurin fasinjojin kamfanin Winfred Ndanu Mutua ta ce, babban kuskure ne hakan. Dukkanmu Bil Adama ne, yau cutar na iya barke a kasar Sin, gobe kuma tana iya barkewa a Afrika. A don haka, abin da ya wajaba a yi shi ne, goyon bayan wadanda suke fama da cutar, da tausaya musu.

Daga Mombasa zuwa Nairobi har zuwa Naivasha, wadannan kudin kyauta kamar digon ruwa ne da ya malala, ya taru daga tasoshin layin dogon dake tsakanin Mombasa da Nairobi, wanda ke da tsayin kilomita 600, har kudi ya zama wani kogi. Bayan kwanaki kadan, yawan kudin da aka bayar ya kai fiye da kudin Sin Yuan dubu 230. Daga cikinsu, ma'aikata 'yan Kenya 182 sun ba da Kenyan shilling sama da dubu 100.

Babban manajan kamfanin Li Jiuping ya ce, ba a tilastawa kowa ya ba da kudi ba, dukkansu sun ba da tallafin ne bisa radin kan su. Ya ce hakan ya burge shi sosai. Ya kara da cewa, ma'aikatan jinya a cikin kasar, suna shiga wuraren dake fama da cutar, kuma Sinawa dake ketare na sa ran ba da gudunmawar su don goyon bayan kasar su.

Ya ce muhimmin aiki dake gaban su shi ne, gudanar da aikin su yadda ya kamata, don ingiza bunkasuwar kasar Kenya, da kuma kara dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China