Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kenya ta yabawa kasar Sin dangane da yaki da cutar Corona
2020-02-08 16:38:50        cri

Hukumomi a kasar Kenya, sun ce kasar Sin ta cancanci yabo bisa irin matakan da ta dauka na dakile yaduwar cutar numfashi ta Corona, da kuma yadda take kula da wadanda suka kamu.

Babban sakataren ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar, Sicily Kariuki, ya ce gwamnatin Kenya na yabawa gagarumin aikin da gwamantin Sin da al'ummarta ke yi wajen yaki da yaduwar cutar numfashi ta Corona, musamman yadda take kula da lafiya da tsaron daliban Kenya da al'amarin ya rutsa da su a yankin da cutar ta bulla.

A nasa bangaren, sakataren ma'aikatar harkokin wajen kasar Macharia Kamau, ya ce Kenya ta yaba matuka da namijin kokarin da Sin ke yi wajen dakile cutar da aka ayyana a matsayin annobar da ta shafi duniya baki daya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China