Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana'antun kasar Sin sun gaggauta samar da kayayyakin yakar cutar numfashi
2020-02-11 13:31:13        cri

A 'yan kwanakin nan, masana'antun kasar Sin wadanda ke samar da kayayyakin kashe kwayoyin cuta da na kare lafiyar al'umma sun yi namijin kokarin samar da wadannan kayayyakin da ake bukata cikin gaggawa.

A kamfanin samar da ruwan kashe kwayoyin cuta na Reward dake yankin Shunyi a karkarar birnin Beijing, ko da yake ana jin karar na'urori sosai, ma'aikatan kamfanin suna aiki kamar yadda ya kamata. Mr. Zhao Jianli, wani direktan kamfanin ya bayyana cewa, a ranar 27 ga watan Janairu, wato a lokacin da galibin Sinawa suke hutun murnar bikin bazara, wato biki mafi muhimmanci ga Sinawa, kamfaninsa ya koma bakin aiki, inda ma'aikatansa ke aiki kowace rana ba dare ba rana. Yawan ruwan kashe kwayoyin cuta da suka samar ya samu karuwa da ninki mai yawa.

"Yanzu mun mai da hankalinmu sosai wajen samar da wani nau'in ruwan kashe kwayoyin cuta, yawan irin ruwan da ake samarwa ya kai ton 150 a duk rana maimakon ton 20 a da. Za mu yi kokarin samar da ton 200 a duk rana a cikin mako guda."

Mr. Zhao Jianli ya yi bayanin cewa, sabo da masana'antun samar da kayayyakin da ba a sarrafa ba sun fara aiki, yanzu kamfaninsa na iya samun isassun kayayyakin da ba a sarrafa ba domin samar da ruwan kashe kwayoyin cuta.

Dalilin da ya sa aka koma bakin aikin samar da karin kayayyakin da ake bukata, shi ne, ma'aikatan kamfanin sun koma guraban aikinsu kamar yadda ake fata. A lokacin da ake hutun murnar bikin bazara, wasu ma'aikata, ciki har da wasu kuku da masu sayar da kayayyaki na kamfanin Reward wadanda ba su koma garinsu ba, sun koma layin samar da ruwan kashe kwayoyin cuta. Madam Lv Yan, sakatariyar kwamitin reshen kamfanin Reward na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta gaya wa wakilinmu cewa, duk wadanda suka koma bakin aiki ba su yi korafi ba ko kadan. "Akawai kuku maza da yawa dake cikin ma'aikata wadanda suka koma layukan samar da kayayyakin. Dukkansu sun yi aiki a dare. Sun yi aikin kunshe kwalbobin ruwan kashe kwayoyin cuta. Sannan akwai wasu shugabanni wadanda suke kula da aikin sayar da kayayyaki, su kuma suna aikin loda kayayyakin da ake bukata."

Ana sayar da galibin ruwan kashe kwayoyin cuta da kamfanin Reward na Beijing ya samar a kasuwannin Beijing da na wasu yankunan dake makwabtaka da birnin, sannan kuma ana samar da wasu zuwa birnin Wuhan.

Kamfanin Aitefu na lardin Jiangsu ya kasance kamfanin samar da ruwan kashe kwayoyin cuta mafi girma a duk kasar Sin, yanzu yana kokarin tabbatar da biyan bukatun da ake da su a birnin Wuhan. Mr. Zhang Congju, mataimakin babban direktan kamfanin ya gayawa wakilinmu cewa, a ranar 24 ga watan Janairu, da kamfanin ya samu umurnin komawa bakin aiki don samar da ruwan kashe kwayoyin cuta, ba tare da bata lokaci ba, kamfanin ya samar da akwatunan ruwan kashe kwayoyin cuta dubu 30 cikin kwanaki biyu kawai domin tallafawa birnin Wuhan. Yanzu, kamfanin yana samar wa birnin Wuhan akwatuna dubu 5 kowace rana. An sa ran cewa, a cikin kwanaki 22 masu zuwa, zai samar wa birnin Wuhan akwatunan ruwan kashe kwayoyin cuta dubu 160. Zhang Congju ya kara da cewa, yanzu, kamfanin yana shimfida sabbin layukan samar da kayayyaki guda 4 domin kokarin samar da karin kayayyakin da ake bukata yanzu cikin gaggawa. Mr. Zhang Congju yana mai cewa, "Kamfaninmu ya shimfida sabbin layukan samar da kayayyaki 4 da ake sarrafa su da kwamfuta. A da, ana bukatar ma'aikata 160 a layukan samar da kayayyaki guda 4, amma yanzu ma'aikata 16 kawai ake bukata wajen sarrafa wadannan sabbin layuka. Amma yawan ruwan kashe kwayoyin cuta da za mu iya samarwa zai karu da yawa."

Kamfanin Zizhu na samar da kayayyakin roba na Guilin, wani reshe ne na rukunin harhada magunguna da kayayyakin jinya na kasar Sin. Daga ranar 24 ga watan Janairu, wato ranar da galibin Sinawa suka fara hutun murnar bikin bazara, zuwa 8 ga watan Faburairu, jimillar safar hannu ta roba da ake amfani da su a asibiti da kamfanin ya samar wa kasuwannin kasar Sin ta kai dubu 620. Mr. Liu Jianguo, direktan ofishin rukunin ya gaya wa 'yan jarida cewa, yanzu rukunin yana kokarin samar da karin safar hannu da ake amfani da su a asibiti, ta yadda za a iya biyan bukatun da ake da su a lardin Hubei da sauran sassan daban daban na kasar Sin. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China