Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar AI na taimakawa kokarin yaki da cutar Coronavirus
2020-02-12 12:49:21        cri

Yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar Coronavirus a kasar Sin, wasu kamfanonin kasar suna tallafawa kokarin da fasahar AI, wato fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam.

A baya bayan nan, kungiyar masana kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta ba da shawarar yin amfani da wasu sabbin fasahohi irinsu 5G, da AI don taimakawa aikin dakile yaduwar cutar Corona, musamman ma a fannonin tattara bayanai, da kula da marasa lafiya, da dai makamantansu.

Yanzu a wani wuri da aka kebe don karbar wadanda suka kamu da cutar Corona a cikin asibitin yara na birnin Shanghai, ana amfani da wani robot, wato mutum-mutumin zamani, mai suna Xiao Bai, domin taimakawa likitoci gudanar da aikin jinya. Yin Yong shi ne darektan sashen kula da cutar numfashi na asibitin, wanda ya bayyana mana cewa, kowane likita kan iya kula da mutanen da ake zaton sun kamu da cutar Corona fiye da 20 a kowace rana, inda ya ce amfani da robot din zai rage musu wahalar aiki.

"Da wannan robot, muna iya tattauna dabarun kula da majiyyata cikin sauki. Ba dole ne kwararru su shiga wurin da aka kebe ba. Za su iya magana da likitoci da majiyyata ta fasahar sadarwa ta bidiyo, don sanin yanayin da ake ciki, da tabbatar da matakan da za a dauka."

Sa'an nan, a lokacin da hukumomin kasar Sin suke gudanar da ayyukan hana yaduwar cutar, su kan fuskanci bayanai da alkaluma da yawa da ke bukatar a nazarce su. Don neman taimakawa wannan fanni, kamfanin Tencent na kasar Sin ya samar da wani nau'in mutum-mutumin zamani, wanda ya iya tattara bayanai game da lafiyar jama'a, haka kuma zai iya ba da amsa ga tambayoyin da jama'a suka yi dangane da yanayin dakile annoba. Ni Jie, wani manaja ne mai kula da fasahar AI na kamfanin Tencent. Ya gaya mana cewa,

"Idan an dauki dabarar gargajiya, to, za a je gidaje daban daban don gano wanda ya kamu da cuta. Aikin yana da wahala, kuma zai sa cutar ta kara yaduwa. Don daidaita wannan lamari, muka tsara wannan robot. Bisa taimakonsa, cikin awa daya za mu iya kammala ayyukan da ake bukatar mutane 20 su yi aiki daga safe har zuwa dare. Ta haka mun kara sauri wajen tabbatar da mutanen da suka kamu da cuta."

Wannan sabuwar fasaha, an riga an fara amfani da ita a wasu wuraren kasar Sin. Ga misali, a birnin Zhongshan dake lardin Guangdong, ana amfani da robot din wajen tattara bayanan jama'a don gano wanda ya kamu da cuta. Sa'an nan a Changsha dake lardin Hunan, ana amfani da fasahar wajen amsa tambayoyin da jama'a suka yi.

Wasu kamfanoni masu kula da fasahar Internet su ma sun samar da hidimar ganin likita a kan intanet. Ga misali, kamfanin JD ya gabatar da wata manhajar kula da lafiya, inda tun daga ranar 26 ga watan Janairun da ya gabata, a kan samu mutane kimanin dubu 100 da suka yi amfani da manhajar a kowace rana, domin su yi tambayoyi masu alaka da batun kare lafiya. Ta wannan hanya, an samarwa mutane sauki wajen neman shawarar likita, tare da rage damar samun cunkuso a asibitoci, wanda ya kan kara yaduwar cututtuka.

Ban da wannan kuma, yanzu an gama lokacin hutun bikin bazara a kasar Sin, don haka ana samun kwararar mutane daga kauyukansu, da gidajen iyayensu zuwa wuraren da suke aiki, lamarin da ya sa ake bukatar tantance lafiyar karin mutane a tashoshin jiragen sama da na kasa. Don neman biyan bukatun da ake da su a wannan fanni, an tsara wata fasahar tantance zafin jikin mutum cikin sauri. Zhao Yong shi ne shugaban kamfani mai wannan fasaha, inda ya ce,

"Mun kyautata fasaharmu a fannin binciken fuskar mutum da zafin jikinsa. Ko da mutum ya sanya marufin baki da hanci, da hula, gami da tabarau, za a iya binciken fuskarsa sosai. Mun yi gwajin fasahar a tashar jirgin kasa, kuma kusan ba ta taba wani kuskure ba."

Yanzu an fara amfani da wannan fasaha a wurare daban daban dake birnin Beijing, wadda ta zama daya daga cikin fasahohin zamanin da ke taimakawa kokarin dakile annobar Corona a kasar Sin. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China