Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yaki da cutar Corona ta zama alama ta kawance mai karfi dake tsakanin Sin da Afrika
2020-02-14 12:33:22        cri

Yakin da duniya ke yi da annobar cutar Corona, ya zama wata alama ta kawance mai karfi dake tsakanin kasashen Afrika da Sin.

Kasar Sin ta dade da kasancewa babbar mai ba da gudunmuwa wajen kula da lafiyar al'umma a fadin duniya, musammam a Afrika. Kuma cikin gomman shekarun da suka gabata, kasar Sin ta aike da tawagogin jami'an lafiya masu kunshe da ma'aikatan lafiya 21,000 zuwa Afrika, kuma wadannan ma'aikata sun duba marasa lafiya miliyan 220 a nahiyar.

Bayan barkewar cutar Ebola a Afrika a shekarar 2014, wasu kasashe sun rufe ofisoshinsu na jakadanci tare da kwashe jami'an diflomasiyya da 'yan kasarsu daga kasashe 3 na yammacin Afrika da annobar ta shafa.

A wancan lokacin na fargaba, kasar Sin ta yanke shawarar ci gaba da kasancewa a nahiyar. Gwamnatin Sin ta tura kayayyakin agaji cikin gaggawa, baya ga tawagar ma'aikatan lafiya sama da 1,000 da suka hada da likitoci soji da fararen hula, zuwa yankunan da cutar ta aukawa. Jami'an diflomasiyya da kwararrun ma'aikatan lafiya, sun kasance cikin yakin da al'ummomin da annobar ta shafa har zuwa lokacin da aka shawo kanta.

Wahalhalu suke nuna sahihiyar abota, kuma abotar Sin da Afrika ta jure abubuwa da dama.

Yayin taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU da aka kammala a ranar Litinin, shugabannin kasashe mambobin kungiyar, sun nuna goyon bayansu da yakinin da suke da shi kan gwamnatin kasar Sin da al'ummar a kokarin da suke na dakile yaduwar cutar.

Gwamnatocin da al'ummomim Afrika, sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban. Misali kasar Comoros, daya daga kasashe mafi karancin ci gaba a nahiyar Afrika, ta ba da gudunmuwar kudi Euro 100, kwatankwacin dala 109 ga kasar Sin domin ta yaki cutar. Za a iya ganin kamar wannan adadi ya yi kadan, sai dai, kyakkyawar niyyar kasar Comoros, abu ne da za a jinjina mata sosai.

Kawo yanzu, ba a samu rahoton bullar cutar Corona a nahiyar Afrika ba, duk da cewa kasashen nahiyar sun karbi shawarar hukumar lafiya ta duniya WHO, ta kada sun dakatar da zirga-zirgar jiragen sama tsakaninsu da kasar Sin.

Yayin da ake fuskantar matsalar da ta shafi lafiyar al'umma, nuna yatsa ko fargaba ba zai taimaka wajen samun nasara ba. Aikin gaggawa da ya rataya a wuyan kowa a yanzu shi ne, cin nasara akan cutar ta hanyar zama tsintsiya madaurinki daya.

Da yake tunatar da yadda aka shawo kan annoba daban-daban kamar cutar Ebola ta hanyar hada karfi da karfi, Shugaban zauren MDD Tijjani Muhammad-Bande, ya yi kira da hada hannu da goyon bayan juna ta sigogi daban-daban, yayin da ake fuskantar kalubale.

Domin kawo karshen annobar nan ba da dadewa ba, kasar Sin ta yi namijin kokarin wajen kulawa da wadanda suka kamu da kuma hana yaduwar cutar. Amma kasar Sin kadai ba za ta iya ikirarin samun nasara ba. Tana bukatar taimako da yunkurin al'ummomin duniya.

Kasar Sin na yabawa taimakon da ta samu daga fadin duniya, kuma za ta ci gaba da yayata bayanai da karfafa hadin gwiwa da kasashe cikin adalci da mutunci, domin kiyaye rayuwa da lafiyar Sinawa da kuma bada gudunmuwa ga lafiyar al'ummar yakinta da na duniya baki daya.

Hadin gwiwa na samar da karin karfi. A hankali, za a ci nasara akan wannan mummunar cuta mai kisa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China