Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar kawancen kasashen Larabawa ta yi maraba da gwamnatin hadin kai ta Sudan ta Kudu
2020-02-24 09:42:07        cri
Kungiyar kawancen kasashen Larabawa, ta yi maraba da kafa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa ta Sudan ta Kudu.

Cikin wata sanarwa, Ahmed Aboul-Gheit, Sakatare Janar na kungiyar, ya taya shugabannin Sudan ta Kudu murnar kafa sabuwar gwamnatin, yana mai bayyana yunkurin a matsayin muhimmin mataki na gina ginshikan tsaro da zaman lafiya a kasar.

Ya kuma bayyana goyon bayan kungiyar ga Sudan ta Kudu, wajen aiwatar da sauran ka'idojin yarjejeniyar da aka farfado da ita na warware rikicin kasar, wadda aka rattabawa hannu a shekarar 2018.

Aboul Gheit ya kuma yi kira ga kasashen duniya su ci gaba da goyawa Sudan ta Kudu da al'ummarta baya, domin cimma nasarar tsarin na wanzar da zaman lafiya.

A ranar Asabar ne, Sudan ta Kudu ta kafa gwamnatin hadin kai na wucin gadi, bayan kasar mafi kankantar shekaru a duniya ta shafe shekaru ta na fama da yakin basasa. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China