Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu aikin sa kai na kokarin gabatar da fasahohin kasar Sin na kandagarkin cutar Covid-19 ga al'ummar Iran
2020-03-10 16:40:14        cri





Yanzu haka kasar Iran na cikin wani matsanancin hali na kandagarkin cutar numfashi ta Covid-19. Sai dai a kafofin sada zumunta na kasar, akwai wata kungiyar masu aikin sa kai da ta ja hankalin al'umma, kungiyar da aka yi wa lakabi da "kungiyar taimakon juna ta kandagarkin cutar Covid-19 a tsakanin Sin da Iran".

Madam Chen Binbin, wadda ta taba koyar da harshen Sinanci a birnin Tehran, babban birnin kasar Iran, wadda yanzu haka take karatun digiri na uku a jami'ar Peking, ita ce ta ba da shawarar kafa kungiyar. A yayin da halin da ake ciki a kasar Iran ya kara kamari, ta samu labarin cewa, al'ummar kasar da yawa ba su san yadda za su kare kansu daga cutar ba, abin da ya dame ta sosai. Don haka, a ranar 24 ga watan da ya wuce, ta bullo da shirin kafa "kungiyar taimakon juna ta kandagarkin cutar Covid-19 a tsakanin Sin da Iran", da fatan gabatar da fasahohin da kasar Sin ta samu wajen dakile yaduwar cutar ga al'ummar Iran ta kafofin sada zumunta. Ba da jimawa ba, ta dauki sama da mutane 100 cikin kungiyar, malamar ta ce, "Yadda cutar ke ta yaduwa a kasar Iran ya sa ni damuwa sosai, don haka nake son gabatar da bayanan da suka shafi kandagarkin cutar da muka samu a kasar Sin ga al'ummar Iran. Sabo da yanzu kasarmu ita ce ta fi samun hanyoyin dakile yaduwar cutar. Bayan da na watsa labarin daukar mutanen gudanar da wannan aiki, nan da nan mutane da yawa suka amsa kiran suka shiga kungiyar, kuma da daren ranar muka fara aikin. "

Malama Chen ta ce, kaso 60% na 'yan kungiyar Sinawa ne, a yayin da ragowar kaso 40% mutanen Iran ne, wadanda suke kulawa da tattaro bayanai da fassara su da hada bidiyo da hotuna da kuma yayata su. Kawo yanzu, 'ya'yan kungiyar sun zarce 200, wadanda suka fito daga Tehran da Berlin da ma jihohin Xinjiang da Guangdong da Henan na kasar Sin.

Abalfazl Delkhaste saurayi ne dan kasar Iran, wanda yake koyon harshen Sinanci a jami'ar Shahid Beheshti ta kasar, ya shiga kungiyar ne nan take bayan ya ji labarinta. Ya ce, ya iya hada bidiyo, kuma yana fatan ilmantar da al'ummar Iran fasahohin kasar Sin na kandagarkin cutar. "Sabo da a ganina, kasar Sin ta samu tarin fasahohi da ilmi a wajen kandagarkin cutar, to, abu ne mai kyau idan aka yada fasahohin daga kasar Sin zuwa Iran ta wasu kafofi. Ina kula da aikin hada bidiyo, ina kuma kula da shafinmu na kafar sada zumunta."

Malama Marzieh behradfar, dalibar kasar Iran ce da yanzu haka take dalibta a birnin Zhengzhou na kasar Sin, ita ce kuma ke kula da aikin fassara a cikin kungiyar. Ta ce, duk da cewa, cutar Covid-19 ta haifar da wahalhalu ga kasashen Sin da Iran, al'ummar kasashen biyu sun kara kusantar da juna a sakamakon cutar. Ta ce, aikin fassara a cikin kungiyar ya ba ta damar ba da gudummawarta ga kasarta ta haihuwa wadda cutar ta addaba, kuma yadda Sinawa da dama ke ba da taimakonsu wajen fassara bayanan, shi ma ya burge ta matuka. Ta ce, "Abin ya burge ni sosai. Aikin sa kai ne, kuma ina son in dinga gudanar da shi ba tare da kasala ba, don ba da gudummawata. Za mu tsaya ga wannan aiki, har zuwa lokacin da aka shawo kan cutar a Iran."

Kawo yanzu, ma'aikatan kungiyar sun fassara hotunan bidiyo kusan 20, wadanda wasu daga cikinsu ake ta raba su a kafofin sada zumunta na Iran. 'Ya'yan kungiyar sun ce suna shirin gabatar da karin hotunan bidiyo da kuma fassara karin bayanai.

A kwanan nan, madab'o'i da dama a kasar Sin suna kokarin ba takwarorinsu na kasar Iran kyautar 'yancin wallafa littattafansu da suka shafi kandagarkin cutar Covid-19, don taimaka wa masu karatu a Iran tinkarar cutar. Barkewar cutar, ta sa an hau wata gada da ta hada zukatan al'ummar kasashen biyu. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China