Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanonin ciniki na kasar Sin suna kokarin farfado da ayyukansu
2020-03-13 12:26:11        cri

Li Xingqian, shi ne darektan sashen cinikin waje na ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin, wanda ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kamfanoni masu kula da cinikin ketare na kasar suna kokarin farfado da ayyukansu yayin da ake ci gaba da fama da cutar COVID-19 a duniya.

Mista Li Xingqian, jami'i mai kula da cinikin waje na ma'aikatar kasuwancin kasar Sin, ya bayyana yayin wani taron manema labaru cewa, ko da yake annobar ta sa kamfanoni dakatar da shirin maido da ayyukansu bayan hutun bikin bazara na kasar Sin, lamarin ya sa yawan kayayyakin da ake fitarwa ya ragu, amma ana ci gaba da samun karuwa a fannin fitar da wasu kayayyaki masu kunshe da sabbin fasahohi, gami da bangaren shigo da wasu danyen kayayyaki. Jami'in ya ce kasar ta riga ta dauki wasu matakai don taimakawa raya bangaren cinikin ketare:

"Don rage illolin da annobar ta haifar ga cinikin ketare, an riga an dauki wasu matakai don taimakawa kamfanoni farfado da ayyukansu, ta yadda za su kiyaye bukatun kasuwannin da suke samu yanzu, gami da samar da kayayyakin da aka yi odar su. Zuwa yanzu matakan sun fara amfani, ganin yadda kamfanoni suke maido da ayyukansu cikin sauri, kana sun fara samar da kayayyakin da ake bukata."

Ta la'akari da yadda hukumar lafiyar duniya WHO ta riga ta bayyana cutar COVID-19 a matsayin babbar annobar da ta shafi daukacin kasashen duniya, jami'in kasar Sin ya ce ba za a iya magance illar da annobar ta kawo wa tattalin arzikin duniya ba, musamman a cikin gajeren lokaci. Sai dai a cewarsa, ma'aikatar kasuwancin kasar za ta mai da hankali kan yadda kamfanoni suke maido da ayyukansu, gami da ba su cikakken goyon baya. Li ya kara da cewa,

"Za a sanya tsarin hadin gwiwar kasashe ta fuskar ciniki ya yi amfani, da kara saurin gina yankunan ciniki masu 'yanci. Sa'an nan za a rage ma kamfanonin haraji, da samar musu da karin bashi, don biyan bukatunsu na samun kudi. Za a kara dora muhimmanci kan wasu sabbin hanyoyin ciniki, irinsu cinikin ketare ta shafin Internet, da sayen kayayyaki a wasu manyan kasuwannin da aka kebe musamman domin cinikin ketare."

Li ya ce ma'aikatarsa tana kokarin kyautata tsarin ayyukanta don tabbatar da ingancin bangaren cinikin ketare na kasar, haka kuma za a baiwa kasuwanni cikakkiyar damar yanke shawara kan yadda za a raba albarkatun da ake bukata tsakani kamfanoni daban daban. Li ya ce,

"Sassan gwamnati za su dauki matakai daban daban don saukaka ayyukan shigo da kayayyaki daga ketare. Sa'an nan, za a samar da cikakkun bayanai ga kamfanoni, don wayar musu da kai game da irin kayayyakin da ake bukata a cikin kasuwanni. Ban da haka kuma za a kara mu'ammala da bangarorin ketare, ta yadda za a taimakawa kulla huldar ciniki tsakanin kamfanonin kasar Sin da na kasashen waje."

A karshe jami'in ce ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin za ta sanya kamfanonin kasar su kara fitar da kayayyakin kandagarkin cuta don taimakawa kokarin dakile cutar COVID-19 a duniya. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China