Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Habasha da kamfanin Alibaba sun hada hannu wajen yaki da COVID-19
2020-03-16 09:57:37        cri
Firaministan Habasha Abiy Ahmed, ya ce kasarsa ta hada gwiwa da katafaren rukunin kamfanin cinikayya ta intanet na kasar Sin wato Alibaba, domin bunkasa aikin yaki da cutar COVID-19.

Wata sanarwa da aka fitar, ta ruwaito Abiy Ahmed na cewa, an cimma yarjejeniyar da rukunin kamfanin Alibaba ne, yayin tattaunawarsa da shugaban kamfanin, Jack Ma, da safiyar jiya Lahadi.

Sanarwar ta ce Habasha na yabawa Jack Ma, bisa bayar da kayayyakin gwajin cutar COVID-19 guda 20,000 da makarin fuska sama da 100,000 da kuma litattafan da suka kunshi hanyoyin yaki da cutar, ga kasar ta gabashin Afrika.

Ta kara da cewa, kayayyakin tallafin da ingantaccen ilimi, su ne jigo wajen dakile cutar COVID-19.

Kamfanin Alibaba na da wasu shirye-shirye kasuwanci a kasar Habasha, wadanda suka samu yabo sosai daga jami'an gwamnatin kasar. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China