Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya baiwa Najeriya kyautar kayayyakin yaki da cutar COVID-19
2020-03-24 21:18:42        cri

 

Jiya Litinin, ofishin jakadancin Sin dake Najeriya ya baiwa ma'aikatar lafiyar Najeriya kyautar wasu kayayyakin kiwon lafiya, domin goyon-bayan gwamnatin Najeriya wajen gudanar da ayyukan dakile annobar cutar. Jakadan Sin dake Najeriya, Zhou Pingjian, da ministan lafiyar kasar Osagie Ehanire da sauran wasu jami'an ma'aikatar sun halarci bikin.

Jakada Zhou ya godewa gwamnati gami da bangarori daban-daban na Najeriya saboda goyon-bayan da suke wa kasar Sin a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19, kana kuma ya ce, kasar Sin tana fatan karfafa hadin-gwiwa da Najeriya da samar mata da taimako a fannin dabarun yaki da cutar.

A nasa bangaren kuma, Osagie Ehanire ya taya kasar Sin murnar cimma manyan nasarori wajen ganin bayan annobar cutar, inda a cewarsa, Najeriya na fuskantar babbar barazanar annobar, kuma tana kokarin koyo dabarun kasar Sin wajen yaki da cutar, da karfafawa daukacin al'ummar kasar gwiwa domin hana yaduwar cutar ba tare da bata lokaci ba.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China