Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta dauki matakan hana shigar COVID-19 daga ketare
2020-03-25 10:48:14        cri

Kwanan baya kungiyar dake kula da aikin dakile annobar cutar numfashi ta COVID-19 ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta yi nuni da cewa, a halin yanzu duk da cewa kasar Sin ta riga ta yi nasarar hana yaduwar annobar a cikin kasar, amma tana fama da matsalar sake barkewar cutar a wasu wurare, a don haka dole ne a ci gaba da himmantuwa kan aikin, musamman ma a bangaren hana shigar cutar daga ketare.

Tun bayan da hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta sanar da cewa, annobar cutar numfashi ta COVID-19 za ta yadu a duk fadin duniya a ranar 11 ga wata, a hannu guda kuma kasar Sin tana fama da matsalar shigar cutar daga ketare, masanin yaduwar cututtuka na cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin Wu Zunyou ya bayyana cewa, kawo yanzu kasar Sin ta riga ta kafa shingaye guda uku domin hana shigar cutar daga ketare, yana mai cewa, "Shinge na farko da kasar Sin ta kafa shi ne hukumar kwastam, idan an gano wanda ya kamu da cutar bayan binciken da hukumar ta yi a wurin shiga kasar, nan take za a kai shi zuwa asibiti, shinge na biyu, killace daukacin mutanen da suka dawo kasar daga ketare a wuraren da aka kebe har tsawon kwanaki 14 domin ci gaba da tantance lafiyarsu, na uku, likitocin asibiti za su tantance wadanda ake zaton sun kamu da cutar."

Wu ya kara da cewa, kasar Sin ta fi sauran kasashe fahimtar cutar COVID-19, saboda ta gamu da yaduwarta kafin sauran kasashe, lamarin da ya sa kasar Sin ta samu fasahohin dakile annobar bisa tushen kimiyya, haka kuma fasahohin za su taimaka wa sauran kasashen duniya yayin da suke kokarin dakile annobar, ya ce, "Muhimman fasahohin dakile annobar da kasar Sin ta samu sun samar da dabaru masu inganci wajen yana yaduwar cutar, mun riga mun fassara dabarun zuwa harshen Turanci domin karin kasashen duniya su yi amfani da su yayin da suke dakile annobar, hakika abu mafi muhimamnci a aikin hana yaduwar annobar shi ne raba mutanen da suka taba kwayar cutar da mutanen da ba su taba da kwayar cutar ba, daukacin kasashen duniya suna iya daukan matakan da suka dace bisa hakikanin yanayin da suke ciki, shi ya sa wasu kasashe suna tambayar mu yadda muke daukan matakan hana yaduwar cutar, wasu kuwa suna koyon dabarunmu."

Kana magungunan sha na gargajiyar kasar Sin suna taka babbar rawa kan aikin dakile annobar a kasar Sin, Wang Rongbing,likitar asibitin Ditan na birnin Beijing ta bayyana cewa, kasar Sin tana son samar da fasahar maganin gargajiyar kasar ga sauran kasashen duniya, tana mai cewa, "Hakika ya zuwa yanzu, mun samu sakamako a mataki na farko yayin da muke kokarin dakile annobar COVID-19 ta hanyar yin amfani da magungunan gargajiyar kasar Sin, muna son hada kai tare da likitocin sauran kasashen duniya domin ganin bayan annobar na da nan, kana muna son samar da dabarun kasar Sin da fasahohin likitancin gargajiyar kasar Sin ga sauran kasashen duniya."(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China