Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
WHO: Annobar COVID-19 ta yi sanadin rayuka sama da 30,000 a duniya
2020-03-30 09:41:22        cri
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu a duniya baki daya, sanadiyyar cutar COVID-19 ya karu zuwa 30,105 ya zuwa jiya Lahadi,

Rahoton hukumar WHO ya ce jimilar mutane 638,146 ne aka tabbatar sun kamu da cutar, inda 555,790 daga cikinsu ke wajen kasar Sin. Kana Amurka ta bada rahoton samun mutane 103,321 da suka kamu da cutar.

Baya ga haka, kasashen da cutar ta fi shafa wato Italiya da Spaniya da Jamus da kowannensu ke da mutane sama da 50,000 da suka kamu da cutar, ya zuwa yammacin jiya Lahadi, akwai jimilar mutane kusan 220,000 da suka harbu.

A nahiyar Turai, da ta zama inda cutar ta fi kamari a duniya, sama da mutane 20,000 sun mutu, kuma daga cikinsu, 2,753 sun mutu ne cikin sa'o'i 24 kafin safiyar jiya Lahadi.

Rahoton ya kuma nuna cewa, an samu yaduwar cutar a cikin gida a kasashe 148. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China