Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masanin Amurka: Cewar COVID 19 ta samo asali daga Wuhan kuskure ne
2020-03-30 10:46:56        cri

Kwanan baya, farfesa Robert Garry na jami'ar Tulane dake kasar Amurka, ya zanta da manema labarai na kafar ABC, inda ya bayyana cewa, kasuwar sayar da naman teku dake birnin Wuhan ba ita ce asalin cutar COVID-19 ba.

 A cikin zantawar tasu, Gary ya cewa, ko da yake, mutane da dama na ganin cewa, kwayar cutar ta samo asali ne daga wata kasuwa dake birnin Wuhan, amma wannan ra'ayi ne mai cike da kuskure. A cewarsa, bincike da yake yi, da sauran nazari da aka yi na nuna cewa, wannan cutar ta samo asali ne daga wani wuri daban, kuma ba shakka akwai mutanen da suka kamu da cutar a Wuhan, amma ba nan ne mafarin cutar ba.

Gary ya kuma kara da cewa, irin wannan kwayar cuta da ba ta kawo illa mai tsanani, ta yadu a tsakanin Bil Adama cikin gommn shekaru.

Ban da wannan kuma, Gary ya ce, daga bincike kan sauran irin wannan kwayar cuta an gano cewa, wannan kwayar cuta na iya sauya halayenta, daga bisani ta zama mai saurin yaduwa, wanda hakan ne dalilin saurin yaduwar COVID-19 a halin yanzu.

Dadin dadawa, rukunin masu bincike karkashin farfesa Gary, ya ba da sakamako cikin bayanin da ya wallafa a kan mujallar "Nature Medicine" cewa, kwayar cuta ta COVID-19 na bulla ne daga indallahi. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China