Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masu aikin jarida na Masar sun yabawa jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron kolin G20
2020-03-30 12:00:21        cri

A yayin taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 da aka shirya musamman a ranar 26 ga wata kan batun tinkarar cutar numfashi ta COVID-19, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabin da ya janyo hankulan masu aikin jarida na kasar Masar sosai. A kwanakin baya, a lokacin da suke yin intabiyu da wakilanmu dake kasar Masar, sun bayyana cewa, shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping ya gabatar sun yi daidai da tunanin raya wata "al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama". Kasar Sin ta gabatar da misalai masu amfani ga sauran yankunan duniya.

Mahmoud Saad Diab, dan jaridar "Al-Ahram" ta kasar Masar mai kula da harkokin kasa da kasa. A shekarar 2019, ya yi watanni 10 yana dubawa da kuma rangadi a kasar Sin domin kara sanin al'ummomin Sinawa. Mahmoud ya ce, a cikin wadannan watanni 10 da ya shafe a kasar Sin ya fahimci cewa, gwamnatin kasar Sin tana da nagartaccen karfin daidaita rikice-rikicen da su kan faru ba zato ba tsammani.

"Bisa hakikanin halin da ake ciki yanzu, cutar COVID-19 ta zama wani iftila'i dake shafar duk duniya baki daya. A hakika dai, a lokacin da ake dakile annobar, ya kamata a yi koyi da fasahohin da kasar Sin ta samu. A cikin shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin ta dukufa kan kokarin daidaita harkokin da suke da nasaba da duk duniya gaba daya. Ya zuwa yanzu, dukkan goyon baya da tallafi da kasar Sin ta samar suna amfanawa kokarin bunkasa duniyarmu sosai."

Mahmoud ya kara da cewa, shawarwari hudu da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron kolin G20 da aka shirya kwanan baya, sun yi daidai da tunanin raya wata "al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'adama". Yanzu abun da ya fi muhimmanci da ya kamata gamayyar kasa da kasa su yi shi ne karfafa niyya da kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa domin dakile cutar kamar yadda ake fata.

A yayin wannan taron musamman na shugabannin kasashe mambobin kungiyar G20 da aka shirya bisa jigon tinkarar cutar COVID-19, an kuma tattauna kan yadda za a bunkasa cinikayya da tattalin arziki a lokacin da ake tinkarar cutar. Mahmoud ya ce, ya amince da shawarwarin kara yin musayar bayanai game da cutar da kuma tabbatar da bunkasa tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasa da kasa kamar yadda ya kamata da shugaba Xi Jinping ya bayar a yayin taron. Mr. Mahmoud ya bayyana cewa, bisa halin da ake ciki yanzu, hadin gwiwar da kasashen Masar da Sin suke yi wajen dakile cutar ta alamta dangantakar sada zumuncin da ta dade tana kasancewa tsakanin kasashen biyu.

Fatma Badawy ta dade tana aiki da jaridar Akhbar Al-Youm ta kasar Masar. Bayan barkewar annobar, jaridar Akhbar Al-Youm ta wallafa rahotanni da bayanai sosai kan yadda kasar Sin take tinkarar annobar. A ganin Fatma, jawabin da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin taron kolin G20 ya burge ta sosai. Matakan da kasar Sin ta dauka wajen shawo kan annobar cikin gajeren lokaci sun zama abin koyi ga sauran kasashen duniya.

"Ina ganin cewa, shugabannin gwamnatin kasar Sin sun jagoranci al'ummar kasarsu sun cimma nasara sosai wajen shawo kan annobar COVID-19 cikin gajeren lokaci, wannan ya zama misali ga sauran kasashen duniya wajen tinkarar annobar da suke fuskanta yanzu. Kasar Sin tana sahun gaba wajen tinkarar annobar, kyawawan sakamakon da kasar Sin ta samu, kuma ya samu amincewar sauran kasashen duniya wajen shawo kan annobar ya zama misalin da ba a taba ganin irinsa ba a da."

Malama Fatma ta kara da cewa, a cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya sake nanata wajibcin kara yin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, kuma ya gabatarwa duniya alamarsa a bayyane sosai.

"A cikin jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya nuna cewa, 'cuta wadda ba ta san kan iyakokin kasa da kasa ba, abokiyar gaba ce ta daukacin bil Adama', wannan takaitaccen furuci ya gaya mana muhimmin dalilin da ya sa dole ne a yi hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa. A ganina, aikin nazarta da kuma yada ilmomin rigakafi da shawo kan annobar da shugaba Xi ya ambata a cikin jawabinsa, abu ne mafi muhimmanci da ya kamata kasashen duniya su yi cikin hadin gwiwa."

Daga karshe dai, Fatma ta kara da cewa, bayan wannan taron shugabannin kasashe mambobin G20 musamman kan batun dakile cutar COVID-19, kokarin cimma matsaya daya tsakanin kasa da kasa kan yadda za su kara yin hadin gwiwa wajen dakile cutar shi ba zai shafi harkokin diflomasiyya da na tattalin arziki kawai ba. Idan ba a so a yi hadin gwiwa da sauran kasashen duniya, shi kansa ba zai kasance a duniya kamar yadda ake fata ba, kuma ba zai ci gajiya ko kadan ba nan gaba. (Sanusi Chen)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China