Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta ci gaba da tattaunawa da kasashen dake son odar kayayyakin kandagarkin COVID-19
2020-03-30 20:00:23        cri
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying, ta bayyana kudirin kasarta na ci gaba da tattaunawa da kasashen duniya, don ganin an magance duk wasu matsaloli da aka iya kunno kai daga tushe, bayan da kasashe da dama suka yi odar kayayyakin kiwon lafiyar kandagarkin cutar nunfashi ta COVID-19 daga kasar Sin, tare da fatan sauran kasashe ba za su sanya batun siyasa a cikin wannan batu ba.

Madam Hua wadda ta bayyana haka yau, yayin taron manema labarai ta ce, har yanzu dai kasar Sin ba ta samu wani korafi daga kasashen ketare da suka sayi kayayyakin kiwon lafiya daga Sin ta kafofi na diflomasiya ba.

Ta ce, kasashen da suka gabatar da wani koke, ofisoshin jakadancin kasar Sin dake irin wadannan kasashen ketare, nan da nan sun gudanar da bincike tare da mayar da daidaita matsalolin.

Matsalar da kasar Slovakia ta gabatar bayan amfani da na'urorin gwajin da ta saya, sun faru ne sakamakon kuskuren da aka samu daga bangaren ma'aikatan lafiyar kasar. Kuma ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar ta Slovakia, ya sanar da ma'aikatan lafiyar kasar kan wannan batu.

Ita ma ma'aikatar lafiya ta Philippines, ta tabbatar da ingancin kayayyakin gwajin da ta karba, da wasu ma'aikatar suka ba da rahoto, kuma sakamakon gwajin na'urorin da kasar ta Sin ta ba ta gudummawa, daidai ne da sakamakon da na'urorin da WHO suka bayar.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China