Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya dace a yi kokarin amfani da dama ta biyu ta kandagarkin COVID-19 ta hada kai
2020-03-30 21:26:03        cri
Kwanan baya mujallar the Lancet ta Birtaniya ta wallafa wata sharhi, inda ta bayyana cewa, hada kai domin ganin bayan annobar cutar numfashi ta COVID-19 yana da muhimmanci matuka, kana an jaddada cewa, dole ne kasa da kasa su hada kai, ta yadda za a guji sake jefa wasu kasashe masu tasowa cikin mawuyacin yanayi.

Yanzu annobar tana yaduwa cikin sauri a fadin duniya, kuma tana shafar daukacin kasashen duniya baki daya, a don haka ya zama wajibi kasashen duniya su hada kai domin samun nasara tare. Yayin taron kolin G20 da aka kira kwanan baya, shugaban kasar Sin ya yi kira da a kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, haka kuma ya gabatar da shawarwari guda hudu da suka hada da: yin kokari domin ganin bayan annobar COVID-19 a fadin duniya, da gudanar da hada kai tsakanin kasa da kasa domin dakile annobar, da nuna goyon baya ga hukumomin kasa da kasa ta yadda za su taka rawa kan yaki da wannan annoba, da kuma kara karfafa sulhuntawa kan manufofin tattalin arzikin duniya bisa manyan tsare-tsare, duk wadannan sun sa kaimi kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa yayin da suke kokarin dakile annobar, kana sanarwar da aka fitar bayan taron kolin ta amince da shawarwarin matuka.

Kwanan baya babban jami'in hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya nuna takaicin cewa, a cikin watanni biyu da suka gabata, kasashe da dama a fadin duniya ba su dauki matakan da suka dace ba, har sun rasa dama ta farko mafi muhimmani ta kandagarkin annobar, yanzu haka ya yi kira ga kasashen duniya da su kara mai da hankali kan batun, kuma su dauki matakai cikin gaggawa, kada su rasa dama ta biyu ta hana yaduwar cutar.

Ko shakka babu shugabannin G20 sun cimma burinsu kan batun yakar annobar, lamarin da zai taimakawa kasa da kasa su yaki annobar.

An lura cewa, kwanan baya shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana yayin da ya tattauna da takwaransa na kasar Sin ta wayar tarho cewa, zai kara mai da hankali kan huldar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, ta yadda sassan biyu za su gudanar da hadin gwiwa a bangaren kandagarkin annobar, ana sa ran zai yi kokari kamar yadda ya yi alkawari.

Masanan kiwon lafiyar jama'a ta kasa da kasa su kan bayyana cewa, ba zai yiyu ba a hana faruwar annoba, amma ana iya hana yaduwarta, a don haka dole ne kasa da kasa su hada kai domin ganin bayanta ba tare da bata lokaci ba.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China