Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sama da mutane 100 sun kamu da COVID-19 a Najeriya
2020-03-31 10:20:32        cri

Cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya (NCDC) ta ce, sama da 100 ne suka kamu da cutar numfashi ta COVID-19 a jahohi 12 na kasar, cibiyar ta bada rahoton jimillar mutane 111 wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar.

Cibiyar ta NCDC ta fitar da sanarwa a Abuja cewa, a ranar Litinin an samu sabbin mutane 14 da suka kamu da cutar COVID-19 a Legas, cibiyar kasuwancin kasar da Abuja, babban birnin kasar.

A Legas an samu sabbin masu kamuwa da cutar 9, yayin da aka tabbatar mutane 5 sun kamu da cutar a Abuja.

A bisa dukkan alamu, Legas, birni mafi yawan jama'a a Najeriya shi ne yake da mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar a kasar. Bayan da aka samu karuwar mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar, a halin yanzu jihar Legas tana da mutane 68 da suka kamu da cutar, yayin da Abuja ke da mutane 21.

Daga cikin jahohin Najeriya 10 da aka samu wadanda suka kamu da cutar COVID-19, akwai jahohi 3 daga shiyyar arewacin kasar.

Mafi yawan rahotannin da aka samu na kamuwa da cutar mutanen da suka shiga kasar ne daga kasashen ketare. Sai kuma mutanen da suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar, a cewar hukumar ta NCDC.

Bayan halin da aka shiga na samun karuwar wadanda suka kamu da cutar, gwamnatin Najeriya ta dauki matakan yaki da annobar, matakan sun hada da rufe dukkan iyakokin shiga da fita kasar da haramta zirga-zirgar jiragen sama daga kasashen waje zuwa kasar. Kawo yanzu an dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a cikin gidan Najeriya, da harkokin sufuri ta hanyoyin mota a tsakanin jihohin kasar.

Chikwe Ihekweazu, babban daraktan hukumar NCDC, ya fadawa 'yan jaridu a Abuja cewa, cibiyar dakile yaduwar cutuka ta Najeriya tana aiki tukuru wajen fadada cibiyoyin gwaje-gwajen cutar ta COVID-19 zuwa sassan kasar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China