Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Amurka da Rasha sun tattauna kan cutar COVID-19 da sauran batutuwan da suka shafi duniya
2020-03-31 10:22:18        cri
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun tattauna jiya ta wayar tarho, dangane da kokarin yakar cutar COVID-19 da sauran wasu batutuwan da suka shafi duniya.

Sanarwar da fadar White House ta Amurka ta fitar, ta ruwaito shugabannin sun tattauna kan yanayin da ake ciki da kokarin da ake yi na yakar cutar COVID-19. Sannan sun amince su yi aiki tare, karkashin kungiyar G20 domin cin nasarar yaki da cutar da kuma farfado da tattalin arzikin duniya.

Donald Trump da Vladimir Putin, sun kuma tabo batutuwan da suka shafi kasar Venezuela da kasuwar makamashi ta duniya. Inda suka amince da muhimmancin dake tattare da daidaita kasuwar makamashin ta duniya. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China