Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ba a iya buga gasar Olympic ta bana
2020-04-02 16:12:51        cri

Wasu rahotanni daga kasar Japan sun bayyana cewa za'a iya fafata wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na bana wanda kasar Japan zata karbi bakuncin saboda kasar tana kokarin kawo karshen cutar COVID 19.

A satin daya gabata ne aka bayyana dage wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na Olympic wadda birnin Tokyo na kasar Japan ya shirya karbar bakunci a bana, zuwa shekara mai zuwa, saboda cutar COVID 19 wadda ta tsayar da duk wasu wasanni a duniya.

Tun farko an tsara fara gasar daga ranar 24 ga watan Yulin shekarar nan, amma yanzu za'a gudanar da shi a shekara mai zuwa in ji kwamitin Olympic na duniya haka kuma an dage wasannin Olympic na nakasassu shima zuwa shekarar ta 2021.

Kwamitin Olympic ya ce za a kira gasar da sunan "Tokyo 2020" duk da a shekarar 2021 ake saran gudanar da wasannin saboda basa son a canja lissafin gasar da kuma yadda za'a dinga tunawa da abinda ya faru a wannan shekarar.

A wata sanarwa ta hadin gwuiwa tsakanin kwamitin Olympic da masu shirya gudanar da wasannin ta ce daukar matakin ya zama wajibi ganin yadda annobar coronabirus ta game duniya kuma babu ranar da za'a kawo karshen ta.

A ranar Litinin daraktan hukumar lafiya ta duniya, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce annobar COVID 19 na ci gaba da ruruwa saboda haka dole ne abubuwa da dama su dakata har sai anga abinda hali yayi

Dubunnan mutane ne suka kamu da cutar a fadin duniya a kusan dukkan kasashe, ana kuma samun karin wadanda ke kamuwa da annobar a kowanne lokaci kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta bayyana.

Ba a taba dage gasar Olympic ba a cikin shekaru 124 da akayi ana gudanar da wasannin, illa an taba soke bikin shekarar 1916 da shekarar 1940 da kuma shekarar 1944 a lokacin yakin duniya na daya da na biyu.

Na Yi Zaton Mutuwa Zan Yi Bayan Na Kamu Da COVID 19 – Hudson-Odoi

Matashin dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Collum Hudson-Odoi, ya bayyana cewa ya yi zaton mutuwa zai yi lokacin da likitoci su ka tabbatar ma sa da cewa ya kamu da cutar COVID 19 a kwanakin baya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne a ka bayyana cewa dan kwallon ya 'warke' daga cutar ta COVID 19 wadda ya kamu da ita kwanakin da su ka gabata kuma ya cigaba da rayuwa kamar yadda ya ke yi a baya.

Dan wasan dan kasar Ingila, mai shekaru 19, ya kasance dan kwallon Firimiya na farko da ya kamu da cutar Cobid 19 a farkon watan da ya gabata, inda likitocin kungiyar su ka mayar da hankali wajen ganin ya samu lafiya.

Tun a satin da ya kamu da cutar ya bayyana wa manema labarai cewa ya na cikin koshin lafiya kuma ya na bin umarnin likitocin kungiyar domin ganin ya warke kamar yadda ya sake wallafa wa a shafinsa na sada zumunta na Instagram.

"Na yi zaton ba zan tashi ba, mutuwa zan yi bayan da a ka gaya min cewa Ina dauke da cutar, saboda yadda na ke jin tsoro da kuma yadda na ke ganin mutane su na mutuwa bayan sun kamu da cutar a kasashe daban-daban," in ji Hudson Odoi

Kungiyar Chelsea wadda dan wasan yake bugawa wasa tana mataki na hudu a kan tebur lokacin da aka dakatar da gasar firimiya a ranar 13 ga watan Maris sai dai alamu sun nuna cewa abu ne mai wahala a iya dawowa domin cigaba da buga gasar saboda annobar cutar Coronabirus da ta dakatar da gabadaya wasanni a duniya.

Har Yanzu Real Madrid Na Bukatar Pogba – Solari

Tsohon kociyan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Santiago Solari, ya bayyana cewa duk da cewa kungiyar ta fara hakura da zawarcin dan wasa Pogba amma har yanzu idan kungiyar ta saye shi zai bata abinda take bukata.

A ranar Lahadi ne aka bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta dakatar da zawarcin da take yiwa dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Paul Pogb, saboda tsoron cutar Coronabirus wadda ta addabi duniya a wannan lokacin.

Sakamakon halin rashin kudi da wasu daga cikin kungiyoyim suka shiga inda ta kai wasu 'yan wasan ma suna yafe albashin da ake biyansu yasa Real Madrid zata tsuke bakin aljihunta idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa.

Ana ganin Real Madrid zata shiga kasuwa a karshen kakar wasa ta bana domin sayen 'yan wasan da zasu karawa kungiyar karfi bayan da tawagar ta Zidane ta sayi dan wasa Edin Hazard amma har yanzu bai bugawa kungiyar abin kirki ba.

Sakamakon annobar cutar Coronabirus yasa Real Madrid ta dakatar da zawarcin da take yiwa Paul Pogba din saboda tana tunanin babu tabbas idan za'a kammala kakar wasa ta bana sakamakon cutar kuma idan ba'a kammala ba za tayi asarar kudi.

Dan wasan tsakiya dai shine wanda Real Madrid take nema ruwa a jallo a wannan lokacin bayan da 'yan wasan ta guda biyu da suka hada da Luca Modric da Toni Kroos gaba daya shekaru suka fara yi musu yawa basa kokari kamar shekarun baya.

Shugaban gudanarwar kungiyar ta Real Madrid, Florentino Perez, ya bayyana cewa abune mai wahala su iya sayen dan wasa Pogba akan farashin Manchester United saboda yayi tsada sannan kuma kungiyar tana ci gaba da yin asara saboda cutar Coronabirus.

Pogba dai bai bugawa Manchester United wasanni ba a wannnan kakar saboda yawan ciwon daya samu a bana kuma gaba daya bai buga wasa ba a wannan shekarar ta 2020 amma ana ganin idan an dawo daga hutun kwallon kafa zai fara wasa.

Yakamata A Ba Wa Liberpool Firimiya, Cewar Gundogan

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Ilkay Gundogan, ya bayyana cewa, adalci ne idan a ka bai wa Liberpool kofin Firimiya na bana, idan har ba a kammala wasannin shekarar nan ba, saboda Coronabirus.

An dai dakatar da gasar firimiya ta Ingila, wadda ake sa ran ci gaba da fafatawa ranar 30 ga watan Afirilun shekarar na ta 2020 sai dai tuni aka shiga shakkun ko za'a iya gama gasar ta bana ko ba za'a iya gamawa ba.

Liberpool wadda rabon ta da kofin firimiya tun bayan shekara 30, tana ta daya a kan teburin bana da tazarar maki 25 tsakaninta da ta biyu wato Manchester City kuma wasanni biyu kacal kungiyar take bukata ta lashe gasar ta bana kuma acikin wasanni biyun zata fafata da abokiyar hamayyarta Eberton sannan ta karbi bakuncin Crystal Palace.

Ranar uku ga watan Afirilu ne kungiyoyin firimiya za su tattauna ko za a sake daga gasar bana a lokacin ko kuma da damar ci gaba da ita idan coronabirus ta yi sauki sai dai abune mai wahala a iya ci gaba da gasar a wannan watan.

A karshen mako ne shugaban hukumar kwallon kafar Turai, Uefa, Aleksander Ceferin ya ce sai dai a soke kakar shekarar nan idan har ba a ci gaba da wasanni a karshen watan Yuni ba saboda babu lokaci.

Sai dai Gundogan ya bayyana cewa idan har za'ayi adalci sai dai a bawa Liberpool gasar ta bana saboda tayi duk abinda za tayi domin ganin ta dauka kuma rashin bata kofin zai lalata karsashi da kwarin guiwar kungiyar.

Manchester United Na Cigaba Da Zawarcin Saul Niguez

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana ci gaba da samun kwarin guiwar sayan dan

wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, Saul Niguez, dan asalin kasar Sipaniya,wanda ya ke buga wasan tsakiya.

Dan wasan tsakiya shine wanda Manchester United zata mayar da hankali idan an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta wannan shekarar inda tuni aka fara danganta kungiyar da 'yan

wasan tsakiya daban-daban a duniya.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana Manchester United ta hakura da zaman Paul Pogba kungiyar wanda hakan yasa ta fara zawarcin dan wasan tsakiyar da zai maye mata gurbinsa

kuma Saul Niguez kociyan kungiyar, Ole Gunner Solkjaer yake ganin zai iya yi masa wannan aikin.

An bayyana cewa Manchester United ta tura wakilanta domin kallon wasan Atletico Madrid da Liberpool a wasan da suka fafata a gasar cin kofin zakarun turai na bana inda Atletico Madrid ta samu nasara har filin wasa na Anfield.

Saul, mai shekara 25 a duniya ya kusa buga wasa na 300 a kungiyar ta kasar Sipaniya saboda tun yana matashin dan wasa ya fara bugawa kungiyar wasa kuma yana da ragowar kwantiragi a kungiyar wanda zai kaishi har shekara taa 2026.

Sai dai farashin dan wasan fam miliyan 135 kamar yadda yake a doka inda tuni aka bayyana cewa Manchester United ta shirya biyan wannan kudi idan har dan wasan zai amince ya koma kungiyar da buga wasa a kakar wasa mai zuwa.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China