Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yusuf Yakub ya karyata jita-jita kan gudunmawar da Sin ta bayar
2020-04-05 20:58:40        cri

Shugaban kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar wakilan Najeriya Yusuf Buba Yakub, ya karyata jita-jitar da ake bazawa game da gudunmawar da kasar Sin ta bayar.

Cikin wata sanarwar da ya fitar kwanan nan, Buba ya ce, tun bayan da aka samu barkewar annobar COVID-19, ana ta yada jita-jita iri daban daban. Daga cikin irin jitar-jitar da ake bazawa akwai wasu dake cewa kayayyakin tallafin da kasar Sin ta bayar suna dauke da kwayoyin cuta. Inda ake yada cewa wai makasudin tallafin kayayyakin da kasar Sin ta bayar ta yi hakan ne da nufin yada cutar numfashi ta COVID-19 a duniya. A cewar Yusuf Buba Yakub, wadannan bayanan karya da ake yadawa suna iya yin mummunan tasiri kan aikin dakile cutar numfashi ta COVID-19 a Najeriya da kuma bata dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin, kuma zai iya bata ran masu bayar da tallafin, kana zai iya lahanta zaman rayuwar al'ummar Sinawa dake zaune a Najeriya. Ya ce Najeriya na bukatar yin hadin gwiwa da sauran kasashen duniya don yin aiki tare da nufin dakile annobar ta COVID-19. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China